Me ka ke nema?


Shafin Farko

Jama'iyyar NPN


Gabatarwa

NPN, Jama'iyyar siyasa ce da aka taɓa yi a cikin jamhuriya ta biyu a Najeriya. Wannan jama'iyyar siyasa ita ce ta zama babbar jama'iyyar da ta tattara tsofaffin 'yan kishin ƙasa, kuma gogaggu a harkar siyasa da mulki; ita ce jama'iyyar da ta lashe mafiya rinjayen kujerun da aka kaɗa ƙuri'u a zaɓen da aka gudanar a shekarar 1979 a ƙasar, da kuma wanda aka sake yi a cikin shekarar 1983. Wannan jama'iyya ta wanzu iya tsawon ran jamhuriyar Najeriya ta biyu; 1978 - 1983.

Asali

NPN, jama'iyya ce da ta samo asali daga wata ƙungiyar kishin ƙasa mai suna National Movement a Turance, wacce kuma Muhammad da Isma'il (2003), suka fassara ta da "Ƙungiyar Kishin Ƙasa". Ƙungiya ce da ta bayyana a lokacin da ake gudanar da zaman Majalisar Nazarin Sabon Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1979.

Yakasai (2012), ya ce, wasu jami'an gwamnatin Najeriya na wannan lokacin da suka haɗa da Shehu Musa 'Yar'aduwa, shugaban ma'aikata na majalisar ƙoli ta soja; Dakta I. D. Ahmad, Kano; Dakta Sule Kumo, Alhaji Abatemi Usman, Farfesa Iya Abubakar da kuma Malam Adamu Ciroma, su suka samar da tunanin kafa wannan ƙungiya. Amma a ruwayar Muhammad da Isma'il (2003), ya zo cewa wasu 'yan majalisar nazarin sabon tsarin mulkin Najeriya na 1979 da aka gudanar a 1978, a zamanin mulkin soja da janar Olusegun Obasnjo ya shugabanta, su suka kafa wannan ƙungiya wacce Farfesa Nwabuze ya shugabanta, Alhaji Shehu Shagari kuma ya yi wa sakatare. Wannan ƙungiya, ita ce ta rikiɗe ta zama jama'iyyar siyasa ta NPN.

Tun da farko, ƙungiyar ta riƙa gudanar da tarurrukan tattaunawa a Festac da ke Legas a Najeriya. Daga baya kuma ta yi wani taron wakilai a jahar Kano, taron da da farko ya samu waigi daga gwamnatin tarayya ta hanyar hana taron da babban jami'in 'yansandan Najeriya M.D. Yusuf ya yi. An so gudanar da wannan taro a gidan Alhaji Mahmud Gashash da wakilai goma-goma daga jahohin Arewa guda goma a wancan lokacin, amma hakan bata samu ba, aka rage yawan mahalarta taron tare kuma da canja muhalin yin taron inda aka yi shi a gidan Alhaji Ahmad Rufa'i Magajin Garin Misau da ke Sabuwar Ƙofa a garin na Kano.

Canjin Suna

A wani taro da mambobin wannan ƙungiya suka gudanar a garin Satelite da ke Legas, aka canja wa wannan ƙungiya suna ta tashi daga Ƙungiyar Kishin Ƙasa ta koma Jama'iyyar Ƙasa ta Najeriya; National Party of Nigeria (NPN). A wannan taro aka zaɓi Alhaji Aliyu Makaman Bidda a matsayin shugaban riƙo, Dakta Ibrahim Tahir kuma a matsayin sakataren riƙo. Sannan kuma aka fitar mata da taken jama'iyya na Ƙasa Ɗaya, Al'umma Ɗaya (One Nation, One Destiny).

Manufofi

Manya-Manyan manufofin Jama'iyyar NPN su ne:

  • Bayar da fifiko a kan bunƙasa noma;
  • Yalwata muhalli;
  • Kyautata ilimi;
  • Gina babbar ƙasa mai cikakken haɗin kan jama'a;
  • Samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali;
  • Bunƙasa tattalin arziƙi;
  • Kyautata jin daɗin jama'a;
  • Kula da harkar lafiya ta hanyar gina asibitoci da samar da magani a asibitocin, da kuma;
  • Kyautata dangatakar Najeriya da ƙasashen ƙetare, da sauran su.

Rijista

Bayan cire takunkumin siyasa da aka yi a ranar 22 ga watan Disamba na shekarar 1978 tun bayan juyin mulkin 1966, jama'iyyar NPN ta samu damar miƙa buƙatar ta ta neman a yi mata rijista ga hukumar zaɓen Najeriya ta wannan lokacin, wato FEDECO wacce ke da cikakken suna na Federal Electoral Commission, wanda kuma aka samu nasarar yin hakan. Wanna shi ne abin da ya baiwa NPN cikakkiyar damar tsayawa takara a dukkan zaɓuɓɓukan da aka gudanar a shekarar 1979 da kuma 1983.

Rabon Muƙamai

Wannan sabuwar jama'iyya ta fito da salon rarraba manyan muƙaman gwamnati da na jama'iyya zuwa shiyya-shiyya a ƙasar ta Najeriya. Rabon ya kasance kamar haka: Jahohin Arewacin Najeriya guda goma (9) aka basu kujerar shugaban ƙasa, Jahohin yamma guda biyu (Anambra da Imo), aka basu kujrara mataimaki, su kuwa jahohin Yamma (5) aka basu shugabancin jama'iyya. Sai kuma ƙananan ƙabilu aka basu shugancin majalisun dokoki da ta dattawa.

Babban Taro

Babban taro a siyasance shi babban taron ƙasa da ake gudanarwa na jama'iyya wanda ake zaɓa mata kodai shugabanni na ƙasa, ko kuma 'ɗan takarar shugaban ƙasa. An gudanar da wannan taro na zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa daga ranar 7 zuwa 9 na watan Disambar 1978 a jahar Legas a ƙarƙashin shugabancin shugabanta na riƙo, Alhaji Aliyu Makaman Bidda. A wannan taro aka zaɓi Alhaji Shehu Shagari daga jahar Sokoto a matsayin ɗan takara. Sauran waɗanda suka tsaya takarar tare da shi akwai Alhaji Yusuf Maimatama Sule daga jahar Kano, Alhaji Adamu Ciroma daga jahar Borno, Farfesa Iya Abubkar daga jahar Gongogola, Mr. Joseph S. Tarka daga jahar Binuwai, sai kuma Dakta Abubakar Bukola Saraki daga jahar Kwara. Tun kafin taron na Legas, sai da aka gudanar da zaɓen fitar da gwanaye uku a dandalin Murtala (Murtala Square) da ke Kaduna, amma daga ƙarshe aka miƙa sunayen mutane shida kamar yadda aka zayyana.

Daga ƙarshe da aka kaɗa ƙuri’a, an zaɓi Alhaji Shehu Shagari a matsayin wanda ya yi wa jama’iyyar takara, bayan an gudanar yaƙin nemana zaɓe kuma, jama’iyyar ta NPN ta samu nasarar kafa gwamnati.

Rushewa

Juyin mulkin da sojoji suka yi a tarayyar Najeriya a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 1983 bayan sake samun nasarar cin zaɓukan da aka sake gudanarwa a wa’adin zangon mulki na biyu, a cikin jamhuriyya ta biyu, shi ne ya kawo ƙarshen jama’iyyar ta NPN da ma jamhuriyyar ta biyu baki ɗayan ta.

Manazarta


Abubakar A. T.  (2001). Maitama Sule Ɗanmasanin Kano. Ahmadu Bello Uniɓersity Press, Zaria-Nigeria.

Muhammad S. da Isma’il A (2003). Tarihin Shehu Shagari. M and I Publishers, Kaduna-Nigeria.

Yakasai T. (2004). Tank Yakasai, The Story of a Humble Life, An Autobiography, ɓolume I. Goɓerment Printers, Kano-Nigeria.



Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya

Tarihin Najeriya


Jama'iyyun Siyasa


Alamomi da Tambari

Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub