Masarautar Burum

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Masarautar Burumawa


Gabatarwa

Masarautar Burum (Bogghom), masarauta ce da ke cikin ƙaramar hukumar Kanam, a jahar Plateau, a Tarayyar Najeriya. An ƙirƙiri wannan masarauta tare da ƙarin wasu masaratu guda goma a shekarar 2002, zamanin mulkin gwamnan Plateau, Joshua Chibi Dariye da jama'iyyarsa ta PDP.

Burumawa sun ɗauki tsawon shekaru 35, suna fafutikar ganin kafuwar wannan masarauta a yunƙurinsu na kufcewa danniya da binne tarihinsu da masarautar Kanam ta yi yunƙurin aikatawa.

Alhaji Shehu Suleiman, shi ne sarkinta na farko, mai taken, Pankwal Bogghom; wanda ke da ma'ana ta sarkin Burum. Sarkin ne mai daraja ta biyu.Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub