Abba Musa Rimi

Me ka ke nema?


Shafin Farko


Abba Musa Rimi


Gabatarwa

An hafi Alhaji Abba Musa Rimi a ranar 28 ga watan Faburairu na shekarar 1940, a garin Rimi na Jahar Katsina.

Karatu

Alhaji Abba Musa Rimi ya yi ‘Elementary School, Rimi’ daga 1948 zuwa 1951, sannan kuma sai ‘Katsina Middle School’ a shekarar 1952, sannan sai ‘Malumfashi Senior Secondary School’ daga 1953 zuwa 1955, sai kuma ‘Kaduna, Technical Secondary School’ wacce yanzu ta koma ‘Government College’ daga 1955 zuwa 1959.

Gogayyar Aiki

Bayan gama karatuttukansa sai ya fara aiki da kamfanin ‘United African Company’ a matsayin jam’in ciniki ‘sales representative’ daga shekarar 1960 zuwa 1962. Ya bar wannan kamfani ya koma kamfanin taba mai suna ‘Nigerian Tobacco Company’ a matsayin jami’in talla, daga shekarar 1963 zuwa 1965. Yana wannan kamfani na taba har sai da matsayinsa ya kai na jami’in rarraba kaya (distributor) mai kula da yankin Funtuwa. Ya bar kamfanin taba ya koma kamfanin ‘United Bawo Construction Company’ a watan Janairu na shekara 1970, ya shiga wannan kamfani a matsayin sakataren mulki (Administrative secretary) na kamfanin, daga baya aka ɗaukaka darajarsa zuwa manajan mulki (Administrative manager), muƙamin da ya riƙe har zuwa barinsa kamfanin a shekarar 1978.

Mataimakin Gwamna/Gwamna

Kafin zamowarsa gwamnan jahar Kaduna ya riƙe muƙamin mataimakin gwamna Alhaji Abdulƙadir Balarabe Musa tun daga shekarar 1979 har zuwa 1981. Ya gaji kujerar gwamna Alhaji Abdulƙadir Balarabe Musa bayan wata ‘yar taƙaddamar da ta jawo tsige shi a shekarar 1983.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).



Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub