Sheikh Muhammad Sa'ad

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sheikh Muhammadu Sa’ad Ngamdu



Sheikh Muhammad Sa'ad Ngamdu

Gabatarwa

Shehin malami Muhammadu Sa’ad Ngamdu. Mutum ne masanin addini da kuma zamani, sannan kuma gogagge a fannin Alƙur’ani da littattafai (fannin ilimi kenan da suka haɗa da fiƙihu, hadisi, tarihi da sauransu); yana cikin irin mutanen da ake kira masana fannoni (muta-fannin). Allah ya yi masa baiwa da sanin addini da kuma karatun zamani bakin gwargwado. Malami ne da sunansa bai ɓuya ba a fannin wa’azin addinin Musulunci a cikin birnin Maidugurin jahar Barno, da kuma ɗariƙar Tijjaniyya. Shehin malami kuma gwani Muhammad Sa’ad yana ɗaya daga cikin mashahuran masu bada darasin al-ƙur’ani tare kuma da tafsirinsa a cikin garin Maiduguri, sannan yana da katafariyar zawiyyar ɗariƙar Tijjaniyya a garin na Maiduguri, tare kuma da al-majirai masu tarin yawa.

Haihuwa

An haifi Shehin malami Muhammad Sa’ad a ranar 30 ga watan Maris na shekarar miladiyya ta 1941 wanda ya yi daidai da ranar 2 ga watan Rabi’ul Auwal na shekarar hijira ta 1360 a garin Maiduguri helikwatar mulkin jahar Barno, sannan kuma fadar Masarautar Barno. Shi ɗa ne ga marigayi malam Ali Ngamdu. An fi saninsa da Sheikh Muhammad Sa’ad Ngamdi.

Karatu

Shehin malami kuma gwani Muhammad Sa’adu masanin fannoni ne wanda ya fara karatunsa a hannun mahaifinsa Modibbo Imam Sa’adu Ngamdu. Daga baya ya ci gaba da karatu a hannun malamai da dama da suka haɗa da: Malam Mamman Mai-Yara, Malam Umar Gwani na Babbar Tsangaya, Malam Muhammadu Usman Dogo, Malam Hassan Nakafaje, Malam Muhammadu Kafaje, dukkansu a garin Ngamdu.

Sannan kamar yadda aka saba a fagen neman karatu Alƙur’ani, daga baya ya fita zuwa  ƙauyen Sawuri da Biriri, da Babban Gida Tarmuwa. Haka nan ma ya zauna a garuruwan Ngala, Wulga, Gamboru, Bama, da Ngelzarma, duk a fafutikar neman karatun al-ƙur’ani. Waɗannan karatuttuka da kuma gogayyar da ya samu daga baya a fannin al-ƙur’ani ita ta bashi matsayin Gwani (Goni) a wannan fanni.

Sannan kuma idan aka juya fannin ilimi; wato karatun littafai, Shehi Muhammadu Sa’ad Ngamdu kogi  a nan, ya yi karatunsa na littattafai a garuruwan Kano da Sakkwato, da sauran gurare.

Haka nan kuma a fannin karatun zamani ma ba’ar shi a bay aba, ya samu nasarar shiga Makarantar Koyon Harshen Larabci (School for Arabic Studies) da ke Kano a shekarar 1971 zuwa 1973, daga nan kuma sai ‘Borno State College of Legal and Islamic Studies’ da ke Maiduguri daga shekarar 1980 zuwa 1983. Bai kuma tsaya iya nan ba, ya samu shiga jami’ar Maiduguri (University of Maiduguri) a shekarar 1983, karatun da bai samu nasarar kammala shi ba saboda harkokin jama’a da na iyali da suka ci ƙarfinsa.

Gogayyar Aiki

Shehin Malami Muhammad Sa’ad Ngamdi ya yi ayyuka da dama da suka haɗa da:

  1. Karantarwa tare da Tafsiri a ƙarƙashin ƙungiyar Jama’atu Nasir Islam tun daga shekarar 1976.
  2. Ya riƙe muƙamin magatakarda (secretary) na Jama’atu Nasir Islam reshen Barno a shekarar 1982.
  3. Ya samu ɗaukakuwa zuwa muƙamin Murshid a shekarar 1991.
  4. Ya zama babban magatakarda (state secretary general) na Jama’atu Nasir Islam na Jahar Barno a 1995.
  5. Ya zama jami’in yankin Arewa-maso-gabas na Jama’atu Nasir Islma tun daga shekarar 2000 har zuwa yau.
  6. Shi ne ciyaman na NAG ta JNI na jahar Barno.

Wasu Muƙaman da ya Riƙe

Shehin Malami Muhammad Sa’ad Ngamdu ya sha zama mamba a hukumar jin-ɗaɗin alhazai da hukumar ilimi duk a jahar Barno.

Sannan kuma a halin yanzu shi ne shugaban kwamitin duba ƙwarewa da ilimin alƙalai a fannin Larabci na hukumar shari’a (Judicial Service Commission) ta jahar Barno.

Rubutu

Shehin Malami Muhammad Sa’ad Ngamdi marubuci ne, daga cikin littattafan da ya rubuta akwai Al-Khuɗabul Mufida.

Kammalawa

A yanzu haka Shehin Malami Muhammad Sa’ad Ngamdi yana zaune a cikin birnin Maiduguri inda ya ke da zawiyya ta ɗariƙar Tijjaniyya, sannan kuma haɗe da makarantar koyar da karatun al-ƙur’ani da sauran fannonin ilimi. Haka nan kuma yana daga cikin mashahuran malam da ke gabatar da tafsiri da wa’azozi a faɗin jahar Barno dama Najeriya baki ɗaya.

Shafin Tarihi


Mashahuran Mutane



Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub