Tanko Yakasai

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Alhaji Tanko Yakasai, CFR



Alhaji Tanko Yaksai, CFR

Gabatarwa

Alhaji Salihu Abukakar Tanko Yakasai, OFR, Bahaushen Kano ne sannan kuma Bacambe a asali. Musulmi ne shi kuma mabiyin Ɗariƙar Ƙadiriyya. Gogagge ɗan siyasa, jajirtacce kuma cikakken ɗan kishin ƙasa, wanda a lokacin da ake yin wannan rubutu, yana da shekaru 68 yana siyasa (1949 – 2017). Alhaji Tanko Yakasai, kamar yadda aka fi saninsa, makarancin Al-Ƙur’ani ne, sannan kuma masanin sauran fannonin addini bakin gwargwado, kuma ɗan jarida. Haka nan ma kuma a fannin karatun zamani ba a bar shi a baya ba, ya kwashi rabonsa kamar yadda wannan rubutu zai tantance.

Alhaji Tanko Yakasai, mutum ne ɗan fafutikar ƙwatar ‘yanci. Da su aka kafa jama’iyyar talakawa ta NEPU, kuma suka zauna a cikinta daram, tun daga lokacin ƙyanƙyasarta, har zuwa ƙarshen rugujewar jamhuriyya ta farko a Najeriya, wanda hakan ne ya sabauta rugujewar dukkanin wasu jama’iyyun siyasa na wacan lokacin.

Da shi aka yi jamhuriyya ta farko, ta biyu, ta uku da kuma ta huɗu wacce yanzu (2017) ake cikinta. Ya ga juyin mulkin soja na farko, sannan kuma ya ga na ƙarshe a wannan ƙasa ta Najeriya. Yana da gogayayyar fafutikar ƙwatar ‘yanci tun daga gida Najeriya har zuwa ƙasashen ƙetare. Da shi aka samawa Najeriya ‘yanci daga hannun Turawa. Duk wanda ya san wannan suna ‘Tanko Yakasai’, a Najeriya da ƙasashen ƙetare, to a fagen fafutikar ƙwatar ‘yanci ya san shi. Haƙiƙa, akwai darrusan ɗiba a cikin rayuwar wannan bawan Allah.

Wannan tarihi na wannan bawan Allah, an ciro ne daga littafin da shi ya rubuta da hannunsa, wanda aka yiwa take da ‘Tanko Yakasai The Story of Humble Life An Auto Biography’, wanda ya ke juzu’i biyu ne; juzu’in farko yana da shafuka 527, juzu’i na biyu kuma yana da shafuka 487.

Haihuwarsa

An haifi Tanko Yakasai a Unguwar Ƙofar Mata da ke Kanon Dabo a Najeriya, a shekarar 1926. Wato shekarar da Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero ya hau karagar mulkin Kano.

Cikakken sunansa shi ne Salihu Abubakar. Laƙabinsa kuma shi ne Tanko; wanda suna ne da ake sakawa duk wanda aka haife shi a bayan mata biyu a Ƙasar Hausa. Abin nufi a nan shi ne, idan ya zamo mutum namiji, yana da yayye mata guda biyu ko fiye, wanda mace ɗaya ta haifa, to akan yi masa laƙabi da Tanko. A ta nasa ɓangaren kuma ƙari a kan wannan, shi ne cewa shi kaɗai ne ɗa namiji da mahaifansa suka haifa a duniya. Sunan Yakasai kuma, ya shiga laƙabinsa ne daga baya, kasancewa a wannan unguwa ta Yakasai ya girma a hannun wata baiwar Allah mai suna Yaya Boyi, wacce ita kuma maqwabciyarsu ce, sannan kuma qawar mahaifiyar Alhaji Tank ce, saboda haka kamar yadda yake a al’adar Hausa a waancan zamani, idan yaro ya isa yaye akan xauke shi daga gidan mahaifansa a kaishi ko dai gidan kakani maza, mata, ko kuma wasu makusanta. Sunanta na asali kuma shi ne Maryam.

Saboda haka, da an ambaci Tanko Yakasai, ko Alhaji Tanko Yakasai, to duk wanda ke bibiyar al’amuran yau-da-kullum a cikin Najeriya da kuma ƙasashen ƙetare, to ya san wanda ake nufi. Cikakken sunansa kuwa shi ne, Salihu Abubakar, yanzu kuma, ana kiransa da Alhaji Salihu Abubakar Tanko Yakasai, CFR.

Salsalarsa

Alhaji Tanko Yakasai, Bacambe ne shi a asali ta ɓangaren mahaifinsa. Mahaifiyarsa kuma Bafilatana ce. Sunan mahaifiyarsa Hauwa, wacce ta ke haifaffiyar garin Lau ce, amma kuma girman Ibi, duk a cikin jahar Taraba.

Shi kuwa mahaifin Alhaji Tanko Yakasai, mai suna Abubakar, wanda kuma aka fi sani da Barau; sunan da Hausawa da Jukunawa suke kiran ɗan-wabi da shi; wato ɗan da aka haifa bayan ɓari ko kuma mutuwar dukkan ciki ko jaririn da mahaifiyarsa ta samu kafin shi. Shi kuma ɗa ne (mahaifin nasa) a wajen sarkin Chamba, Abdullahi. Chambawa, ɓangare ne na rusasshiyar daular Kwararrafa.

Rikicin ƙabilanci da ke gudana a wannan yanki, shi ne abin da ya saka aka ɗauki mahaifin Tanko Yakasai zuwa garin Laro, wanda a lokacin bai wuce ɗan shekaru 11 ba a duniya. Ya zauna a wannan gari na ɗan taƙaitaccen lokacin da bai kai shekara guda ba inda ya fara koyon karatun Alƙu’ani. Daga baya aka ɗauke shi zuwa garin Gaundare, tare da sauran almajirai dan ci gaba da wannan karatu na Alƙur’ani, inda ya zauna har kusan shekaru biyu a garin. Daga nan kuma suka ƙara gaba zuwa garin Marwa, daga nan ma bayan wani dogon lokaci suka sake ƙarawa gaba zuwa Garwa. Dukkan waɗannan garuruwa, Gaundare, Marwa da Garwa suna cikin ƙasar Kamaru a yau.

Daga ƙarshe, mahaifin Alhaji Tanko Yakasai ya koma garin Yerwa, dan ci gaba da karatunsa na Alƙur’ani. A lokacin zamansa na Yerwa, wacce ke cikin jahar Borno a yau, Allah ya haɗa shi da wani ɗankasuwa mai suna Umaru daga garin Kano, inda a ƙarshe Marigayi Alhaji Abubakar, tare da wannan bawan Allah mai suna Malam Umaru, suka rankaya zuwa Kano, bayan sun ɗauki lokaci suna gudanar da kasuwancinsu a tsakankanin Bauchi da Borno.

Ita kuwa mahaifiyar Alhaji Tanko ta nata ɓangaren, ta auri wani mutum mai suna Malam Musa wanda yake boyi-boyin Turawa ne a garin Ibi, tun kafin haɗuwarsu da Alhaji Abubakar. Daga wannan gari na Ibi suka yi wo ƙaura zuwa Kano tare da mijinta. Bayan dawowarsu Kano, wannan aure nasu da malam Musa ya rabu.

Bayan rabuwar wancan aure na Hajiya Hauwa da Malam Musa, sai kuma Allah cikin hikimarsa ya haɗa ta da shi Alhaji Abubakar, waɗanda dukkansu ‘yan asali jaha ɗaya ne, wato Jahar Taraba kenan a yau. Daga ƙarshe suka yi aure a junansu wanda sanadiyyar wannan aure aka haifi shi Alhaji Tanko Yakasai.

Karatunsa

Bayan cikar Alhaji Tanko Yakasai shekaru huɗu da haihuwa, ya fara karatunsa na Alƙur’ani a shahararriyar Makarantar Karatun Alƙur’ani da ke Gidan Sarkin Gini, a Unguwar Yakasai, Tsohuwar Rimi daga shekarar 1933 zuwa 1937. Sunan shugaban wannan makaranta malam Adamu. Bayan rasuwar malam Adamu sai aka canja wa wannan makaranta matsugunni ta koma kusa da gidan Sarkin Yaƙi wanda aka fi sani da Sani Maiƙira, wanda kuma shi ne mahaifin Alhaji Sani Kwangila.

A cikin shekarar 1935, mahaifin Alhaji Tanko ya saka shi a makarantar elimantare ta Shahuci da ke Kano. Alhaji Tanko bai samu nasarar kammala wannan makaranta ba sakamakon cire shi da mariƙiyarsa wato Yaya Boyi ta yi, ta kuma sake saka shi a wata makarantar karatun Alƙur’ani. Wannan kuma ya biyo bayan ƙyamar karatun boko da mutanen dauri suke da ita, bisa fahimtar cewa, shi karatun na boko zai lalata tarbiyyar yara. Sakamakon haka, sai ya nemi Yaya Boyi ta mayar da shi gaban mahaifansa, a zatonsa, mahaifin nasa zai sake saka shi a wata makantar ta elimantare a garin Harɗawa, garin da mahaifin nasa ya koma da zama daga baya, bisa gayyatar sarkin garin na wancan zamanin. Amma hakan bata samu ba sai aka sake saka shi a Tsangayar Mallam Musa Ɗankore da ke garin Harɗawa, a jahara Bauchi, inda ya sake yin karatun Al-Ƙur’ani daga shekarar 1937 zuwa 1939.

Bayan dawowar su Kano daga Harɗawa, an sake saka shi a makarantar Malam Idi, inda  a nan ma ya yi karatun Al-Ƙurani daga shekarar 1939 zuwa 1940. Wannan karatu ya yi shi a unguwar Tudun Jaba, ta cikin Yakasai, a garin Kano. Sai kuma makarantar Alhaji Balarabe Kofar Mata, da ke Kano, inda ya yi karatun Al-Ƙur’ani da sauran littattafan Musulunci daga shekarar 1940 zuwa 1942.

Zakaran da Allah ya nufa da cara…, Alhaji Tanko Yakasai ya sake komawa karatun zamani a shekarar 1941 lokacin yana da shekaru 15 a duniya (1926 – 1941). Inda ya halarci ajujuwan karatun manya na la’asar (Shahuci Evening School), a makarantar Shahuci, Kano, daga shekarar 1941 zuwa 1946. Daga shekarar 1952 zuwa 1955 kuma, ya halarci darasin Turanci (British Council English Tutorial Classes) da cibiyar yaɗa al’adun Birtaniya (British Council) da ke Kano ta shirya. Sai kuma a shekarar 1956, inda ya yi karatu a fannin ‘Comparative Federalism’ a jami’ar Ibadan, a reshenta na ‘Extra Mural Department’.  Haka nan a shekarar 1959 a dai wannan jami’a ta Ibadan, ya sake halartar wani darasin a fannin ‘Problem of Independence and Development’. Dukkan waɗannan karatuttuka da ya yi, ya fita da takardar sheda mai darajatar ‘Certificate Course’. Daga ƙarshe kuma a cikin shekarar 1963, bayan rugujewar jamhuriyya ta farko, ya samu halaratar makarantar  Wilhem Pieck Youths Higher Institute  da ke garin Bogansee,  na ƙasar German Democratic Republic, (GDR) inda ya yi karatun difiloma a fannin kimiyyar siyasa (Diploma in Political Science) a babbar makarantar Wilhem Pieck Youths Higher Institute.

Shigarsa Siyasa

Alhaji Tanko Yakasai, gangaran ne a siyasa, ya samu cikakkiyar gogayya a siyasa. Ya kwashe shekaru 68 yana siyasa (1949 – 2017). An kafa jama’iyyun siyasa da dama da shi tun daga farkon fara siyasa a Najeriya zuwa yau. Watau daga jamuriya ta farko har zuwa wannan ta huɗu da ake cikinta.

A watan Disamba na shekarar 1949, ya fara halartar taron Jama’iyyar Mutanen Arewa, wacce a lokacin ta ke a matsayyin ƙungiyar walwala da siyasa (socio-political group), taron da aka gudanar a tsohuwar sinimar El-Duniya, da ke daf da kasuwar Kanti Kwari, Kano. Tun daga wanccar shekara ta 1949, zuwa 2002, Alhaji Tanko Yakasai an kafa jama’iyyu da dama da shi, sannan kuma daga baya ya zama ɗan siyasa mai zaman kansa; wato ɗan siyasa maras jama’iyya kamar yadda bayanai za su zo a ƙasa:

  1. A Jamhuriyyar farko, cikin shekarar 1951, Alhaji Tanko Yakasai ya shiga Jama’iyyar NEPU; wacce taƙaitawa ce ta ‘Northern Element Progressive Union’. Ya samu shiga wannan jama’iyya a shekarar 1951. A lokacin da jama’iyyar ta gudanar da babban taronta na ƙasa a sinimar El-Duniya da ke daf da kasuwar Kantin Kwari, Kano a Najeriya. Shigarsa wannan jama’iyya kuma ya biyo bayan hanawar da Turawan mulkin mallaka suka yi na tabbatar da Jama’iyar Mutanen Arewa ta zamanto cikakkiyar jama’iyyar siyasa. Tun daga wannan lokaci, Alhaji Tanko Yakasai yana cikin wannan jama’iyya har zuwa ƙarshen jamhuriyya ta farko a shekarar 1966. Wato kenan, an yi gwagwarmaya da shi na tsawon shekaru 15 (1951 – 1966) a cikin wannan jama’iyya ta NEPU mai farin jini a wajen talaka, sannan kuma abokiyar adawar masu mulki waɗanda suka yaƙe ta da dukkan ƙarfinsu.
  2. >A jamhuriyya ta biyu kuma, wacce ta fara daga 1967 zuwa 1983, ya shiga ƙungiyar siyasa mai suna ‘National Movement’ wacce daga baya ta rikiɗe ta koma jama’iyyar NPN wacce ke da ma’ana ta, ‘National Party of Nigeria.
  3. A jamhuriyya ta uku; mai gajeren kwana, wacce aka fara ta daga shekarar 1992 zuwa 1993, ya shiga jama’iyyar SDP; wacce ke da ma’ana ta ‘Social Democratic Party’.
  4. A jamhuriyya ta huɗu, wacce aka fara ta daga shekarar 1998 zuwa yau (2017), Alhaji Tanko Yakasai, ya zaɓi zama ɗan siyasa mai cin-gashin-kai; wato ɗan siyasa maras jama’iyya. Amma, daga baya abokansa suka gayyace shi, suka haɗa kai, suka kafa jama’iyyar APP. Kalmar APP kuwa, taƙaitawa ce ta ‘All Peoples Party’, jama’iyyar da daga baya ta rikiɗe ta koma ANPP da ma’ana ta ‘All Nigerian Peoples Party’, a ƙarshe kuma ta narke ta koma APC wacce ke nufin ‘All Peoples Congress’, wacce a lokacin da ake wannan rubutu (2017), ita ke riƙe da kujerar shugabancin Najeriya ƙarƙashin shugaba Muhammadu Buhari, wadan kuma Farfesa Yemi Osinbajo yake yiwa mataimaki.

Daga ƙarshe, a cikin shekarar 2002, Alhaji Tanko Yakasai ya fice daga wannan jama’iyya ta APP da aka kafa ta da shi, ya koma ɗan siyasa mai zaman kansa; wato ɗan siyasar da bashi da jama’iyya. Matakin da ya ce ya yi koyi ne da fitaccen ɗan siyasar ƙasar Birtaniya, wato firimiya, Sir Harold Wilson, wanda ya sauka daga kan kujerarsa ta firimiyan Birtaniya bayan an zaɓe shi a karo na biyu. Ya kuma yi haka ne saboda a lokacin shekarunsa sun kai sittin, saboda haka sai ya sauka dan ya huta. Shima a ta nasa ɓangaren, Alhaji Tanko Yakasai tun wancan lokacin ya ƙudurce a zuciyarsa cewa zai bar siyasar jama’iyya idan shekarunsa suka kai sittin. Amma cikin rashin sa’a, a ta naa ɓangaren, daidai lokacin da shekarun nasa suka cikka sittin, an samu tangarɗa, ba a siyasa a Najeriya, lokacin shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ne ke mulki; wato zamanin sojiji ne. saboda haka ya jinkirta sai da dama ta zo masa, sannan ya bari.

Gwagwarmayar Siyasa

Tsawon lokacin da ya ɗauka a yana fafutikar siyasa da ƙwato ‘yancin ɗan’adam, Alhaji Tanko Yakasai ya haɗu da abubuwan da lissafo su ke da matuƙar wahala. Wahalhalu da suka haɗa da muzantawa, musgunawa, rashin abinci da sha musamman lokacin NEPU, tafiyar ƙasa a cikin mawuyacin hali, da kuma uwa-uba ɗauri, suna daga cikin abubuwan da ya fuskanta kuma ya jure, tare kuma da jajircewa a kan abin ya saka a gaba.

Bincike ya tabbatar da cewa, kusan daga shekarar 1953 zuwa 1986, shi ne ɗan siyasar da aka fi ɗaure wa a duk faɗin Najeriya. Ya sha ɗaure-ɗaure ciki kuma har da zaman ƙiriƙiri. An ɗaure sau uku a zamanin Turawa kafin samun ‘yancin ƙasa, sau uku kuma a cikin jamhuriyya ta farko, sai kuma ɗauri biyu da ya sha a hannun gwamnatin sojoji biyu; shugaba Muhammadu Buhari da kuma shugaba Ibrahim Badamasi Babangida, abin da ya kai adadin ɗaure-ɗauren da ya sha zuwa ɗauruka takwas.

Muƙaman da ya Riƙe

  1. 1952 – 1955, ya zama babban sakataren kwamatin matasan NEPU, mai suna “NEPU Positive Action Wing (PAW)”.
  2. 1954 – 1955, ya riƙe muƙamin babban jami’in hulɗa da jama’a      (National Publicity Secretary) na jama’iyyar NEPU.
  3. 1954 – 1956, ya riƙe muƙamin babban ciyaman (National Chairman) na majalisar samarin NEPU (NEPU Youth Association).
  4. 1955 – 1958, babban sakataren jama’iyyar NEPU (National Secretary).
  5. 1959 – 1961, ya riƙe muƙamin babban ciyaman na ƙungiyar samarin haɗakar jama’iyyun NCNC da NEPU (National Chairman, NCNC/NEPU Youth Association).
  6. 1961 – 1962, babban sakatare (Secretary General), na jama’iyyar Sawaba ta Najeriya.
  7. 1961 – 1964, mataimakin babban ciyaman na Majalisar Samarin Najeriya (Deputy National Chairman, Nigerian Youth Congress, NYC).
  8. 1963 – 1966, mataimakin babban sakatare na “Northern Progressive Front”.
  9. 1966 – 1975, mamba na hukumar gudanarwar makarantar al’umma ta Kano (Founding member of Board of Governors, Kano Community Commercial College, KCCC).
  10.  1969 – 1973, ya riƙe muƙamin shugaban reshen Najeriya na Ƙungiyar Goyon Bayan ‘Yan Afirka a Yankin Asiya (Chairman Nigerian Chapter Afro-Asian People’s Solidarity Organization (AAPSO)).
  11.  1970 – 1975, mamba na hukumar gudanarwar asusun ci gaban ilimi na Jahar Kano (Founding member of Governing Council of Kano State Education Development Fund (KSEDF)).
  12.  1971 – 1975, ya zama wakilin Najeriya a kwamatin dokoki na Majalisar Wanzar da Zaman Lafiya ta Duniya (Nigerian Representative on the Executive Committee World Peace Council).
  13.  1974 – 1976, ya riƙe muƙamin babban shugaba na ƙungiyar ƙawancen yaɗa al’adu tsakanin sobiyet da Najeriya (National Chairman Nigeria-Soviet Friendship and Cultural Association (NSFCA)).
  14.  1974/75, wakili a kwamitin tuntuɓa game da taron tsarin mulkin ƙasa (Founder Constitutional Conference Delegates Consultative Forum).
  15.  1975/76, ya riƙe muƙmin babban mai tuntuɓa (National Coordinator) na jama’iyyar siyasa maras rajista ta (Congress for National Consensus (CNC)).
  16.  1977, ra riƙe muƙamin babban mai tuntuɓa (National Coordinator) na Northern Patriotic Front.
  17.  1978 – 1982, ya riƙe muƙamin mataimakin shugaban jama’iyyar NPN na Kano, sannan kuma mamaba na kwamitin gudanarwa na jama’iyyar (Deputy State Chairman, Kano and Member National Executive Committee, National Party of Nigeria (NPN)).
  18.  2003 har zuwa yau (2017), yana riƙe da muƙamin mamba a kwamatin amintattu na Ƙungiyar Dattawan Arewa (Founding member and member Board of Trustees Arewa Consultative Forum, ACF).
  19. 2013/2015, shi ne babban shugaba (National Chairman) na Nigeria National Summit Group.
  20.  2014, ya zama mamba na National Conference Consensus Building Group.

Gogayyar Aiki

  1. 1954 – 1960, ya zama editan Hausa na jaridar ‘Daily Comet’, Kano.
  2. 1966 – 1967, jami’in ciniki na gidan man AGIP Nigeria Ltd, yankin Kano.

Ofisoshin Gwamnati da ya Riƙe

  1. 1967 – 1971         ya zama kamishinan yaɗa labarai na jahar Kano.
  2. 1971 – 1972         ya zama kamishinan ma’aikatar gandun daji, raya karkara da kuma kwafarati (Forestry, Community Dev. and Cooperatives) na jahar Kano.
  3. 1972 – 1975         ya zama kamishinan ma’aikatar kuɗi ta jahar Kano.
  4. 1973 – 1975         ya zama mamba na hukumar gudanarwar babbar makarantar harkokin ƙasa-da-ƙasa (Nigerian Institute of International Affairs) ta Najeriya.
  5. 1979 – 1983         ya riƙe muƙamin mai baiwa shugaban ƙasa shawara da shiga tsakanin majalisar Najeriya.

Tarurrukan Ƙarawa Juna Sani da na Tattaunawa

  1. A shekarar 1956,  ya halarci taron ƙarawa juna sani (conference). Taron da ya tattara dukkan jama’iyyun siyasar arewa, wanda Sir Ahmadu Bello Sardauna ya shirya, Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa kuma ya jagoranci zaman taron. Taron da ya shirya tsare-tsaren karɓar baƙunci sarauniyar Ingila a Arewacin Najeriya.
  2. 1958, ya halarci taron ƙarawa juna sani mai taken “All- Africa Peoples Conference”, taron da aka gudanar a garin Accara, na ƙasar Ghana. A wannan taro aka tsara yarjejeniyar cin-gashin-kan Nahiyar Afrika.
  3. 1960, ya halarci taron Majalisar Matasa ta Duniya (World Assembly of Youths), wanda aka gudanar a garin Tunis, na ƙasar Tunisiya.
  4. A shekarar 1960, ya halarci taron ƙarawa juna sani. Taron da aka yiwa take da, “All-Africa Positive Action Conference against French Atomic Test in the Sahara”. An gudanar da taron a garin Tunis, na ƙasar Tunisiya.
  5. >1960, ya halarci taron ƙarawa juna sani na ƙasa-da-ƙasa (International Conference), wanda aka yi dan goyawa ƙasar Aljeriya baya ta samu ‘yancin kai daga hannun Faransa. An yi wannan taro a garin Peking, na ƙasar Cana (China).
  6. >1967, ya halarci taron wakilan shugabannin Arewa, taron da aka yi a garin Kaduna, da nufin samun matsaya guda kan sha’anin rikicin tsarin mulkin ƙasa na shekarar 1967.
  7. 1967, ya halarci taron kafa kwamitin baiwa gwamnan Yankin Arewa shawara.
  8. 1967, ya halarci taron masu bada shawara na Arewa game da ƙiƙiro sababbin jahohi a Najeriya.
  9. A shekarar 1969, ya halarci taron ƙarawa juna sani wanda aka gudanar dan goyon bayan ‘yan Afirka mazauna Asiya (Afro- Asian Peoples) a garin Khartum, na ƙasar Sudan.
  10.  1970, ya halarci babban taron Majalisar Wanzar da Zaman Lafiya ta Duniya (World Peace Council), wanda aka gudanar a garin Berlin, na jamhuriyar Jamus (German  Democratic  Republic, GDR).
  11.  A shekarar 1994/1995, ya halarci taron ƙarawa juna sani game da tsarin mulkin Najeriya (Nigerian Constitutional Conference).
  12.  2014, ya samu halartar taron ƙasa da aka yi (Nigerian National Conference), a zamanin shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan.
  13.  2014, ya halarci taron “National Conference Consensus Building Group”.

Gudunmawarsa

Alhaji Tanko Yakasai, shi ne mutum na farko da ya fara samarwa da ‘yan’arewa guraben ƙaro karatu a ƙasashen waje ƙarƙashin tsarin tallafin karatu (scholarship), ba tare da saka hannun gwamnati ba. Daga cikin irin mutanen da suka ci gajiyar irin wannan taimako nasa akwai Dr. Muhtari Ahmed Kura, Bello Sule, Malam Sidi Kwaru, Garba Ɗorayi, Ado Gwadabe, Alhaji Muhammad Abubakar Yakasai, da kuma Dr. Muhammed Achimalo Garba, duk daga jahar Kano. Sai su Hamza Ahmed, da Tanko Yaro Mahmud, daga jahar Filato. Akwai Muhammad Nasir Ahmed, daga jahar Sokoto.  Sai kuma Baba Jimeta, daga jahar Adamawa. Sannan akwai Nuhu Muhammed, daga jahar Neja.

Lambobin Yabo da Muƙaman Sarauta

Bisa la’akari da gagarumar gudunmawa da ya bayar a tsawon waɗannan shekaru, kamawa tun daga fafutikar samun ‘yancin Najeriya, har zuwa kan ɗorewar haɗin kan Najeriya, ya cancanci a girmamashi tare kuma da jinjina masa. Kaɗan daga cikin irin muƙamai da aka yi masa dan girmamawa akwai:

  1. A shekarar 1970, ya karɓi kyautar zama uba na din-din-din (Life Patron Award) na ƙungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya reshen jahar Kano.
  2. A shekarar 2013, an yi masa naɗin Ƙauran Ganye, daga masarautar Ganye ta jahar Adamawa, a Najeriya.
  3. A shekarar 2014, an yi masa sarautar Odosiobodo of Ogbunike, daga masarautar Anaca (Onitsha), da ke jahar Anambra a Najeriya.
  4. 2005, ya karɓi lambar girmamawa ta ƙasa, mai taken CFR, wacce taƙaitawa ce ta ‘Officer of the Order of the Federal Republic of Nigeria’, lambar da shugaba Ubasanjo ya bashi.
  5. A shekarar 2007, ya karɓi kyautar grimamawa daga gidan talabijin na tarayyar Najeriya a ɓangaren ciyar da arewancin Najriya gaba da kuma haɗewarsa waje guda (NTA Prominence Award for Northern Development & Integration).
  6. A shekarar 2010, ya karɓi takardar yabo ta mutanen da suka yi nasara, sannan kuma mafiya tasiri a jahar Kano (Kano State Government Achievers Award: Most Influential Personality of the Year).
  7. A shekarar 2013, babbar makarantar harkokin ƙasa-da-ƙasa ta Najeriya (Nigerian Institute of International Affairs) ta bashi takadar yabo ta matsayin mamba na din-din-din (Life Member Award).
  8. A shekarar 2014, ya karɓi takardar yabo a matsayin ɗan siyasar dukkan jamhuriyoyi (National Conference Award of All Time Democrat).

Kaɗan kenan daga cikin irin lambobin yabo da girmamawa da Alhaji Tanko Yakasai ya karɓa.

Iyali

Alhaji Tanko Yakasai mutum ne mai son iyali, ya zuwa lokacin da ake yin wannan rubutu, yana da mata huɗu daga cikin tara da ya aura. Sai kuna ‘ya’yan da yawansu ya kai goma sha tara da jikoki hamsin da bakwai.

Manazarta:


Yakasai T. (2004). Tank Yakasai, The Story of a Humble Life, An Autobiography, Volume I. Goverment Printers, Kano-Nigeria.

Yakasai T. (2004). Tank Yakasai, The Story of a Humble Life, An Autobiography, Volume II. Goverment Printers, Kano-Nigeria.

Tattaunawa da Alhaji Tank Yakasai a Gidansa da ke Lamba 45 Sagir Kumashi Street, Kawaji, Kano. A watan Fabarairu na Shekarar 2017.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub