Kayan Izga
Gabatarwa
Su ne waɗanda ake kaɗawa ko gogawa. A cikinsu akwai: Gurmi, garaya, kuntugi, molo, kwamsa, goge, komo, kukuma da lasha.
Sassan Jikin Kayan Izga
Kusan waɗannan abubuwa da za a zayyano, su ne gama-garin sassan jikin abubuwan kiɗa na izga. Ga su kamar haka:
- Fata: Da ita ake rufa abin kiɗa.
- Izga: Tsirkiya ce, wacce ita ce zaren da ake ɗaurawa daga saman abin kaɗawa zuwa ƙasa. Kuma ita ake kaɗawa da hannu ko da ƙirgi. Saboda haka ma sunan kayan ya samo asali daga nata sunan ake cewa, kayan izga.
- Kallabi: Fata ce da ake ɗaure saman tsirkiya a jikin sanda da ita.
- Sanda: Itace ne maras kauri sannan kuma ɗan dogo wanda baya wuce zira’i ɗaya da rabi. A jikinsa ake zura ƙoƙon gurmi da sauransu, sannan kuma a ɗaura tsirkiya a jikinsa daga sama zuwa ƙasa.
- Farke: Ƙirgi ne, wato busasshiyar fatar saniya ko kuma tsinken gashin ungulu, waɗanda ake kaɗa wasu daga cikin kayan izga da su. Ana kaɗa garaya da komo da farken ƙirgi. Kuntigi kuma da tsinken gashin ungulu ake kaɗa shi.
- Ceba: Ƙarfe ne mai ɗauke da zobban ƙarfe, wanda ake kafa shi a bakin gangar noma.
- ‘ya’yan baba.
- Baka: Itace ne ƙarami ake yi masa sha irin na baka a ɗaura tsirkiya a jikinsa. Ana goga koma, goge, da kuma lasha da shi.
Manazarta:
Gusau S.M. (2017). Kayan Kiɗan Hausa. Centuary Research and Publications, Kano – Nigeria.
Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.
Tattaunawa da Umaru mai gurmi a garin Uke ta jahar Nassarawa a ranar Alhamis 14/3/2018.
Tattaunawa da Sarkin Kiɗan garin Alitini, Isma'ila Namarke, a garin Alitini, ƙaramar hukumar Warawa, a Jahar Kano, Najeriya. A ranar 17 ga watan 6, na shekarar 2017.
Wakokin Makaɗa
- Waƙoƙin Makaɗa
- Makaɗan Fada
- Makaɗan Sarauta
- Makaɗan Jama’a
- Makaɗan Maza
- Makaɗan Mata
- Makaɗan Ban-Dariya
- Makaɗan Sana’a
Kayan Kiɗan Hausa
Tatsuniyoyi
- Gizo da Noman Gyaɗa
- Gizo da Saniya
- Gizo da Ƙoƙi da Kantu
- Gizo da Ɗanrago...
- Gizo Ɓarawon Gyaɗa
- Gizo da Ɓaure
- Biri da Kura
- Kura da Kare
- Auren Barewa...
- Kuturu, Makaho...
- Alhaji da Hajiya
- Wasu Mutane Huɗu
- Baban Rogaji
- Yarinya da Ƙawayenta
- Mutum da Zabi
- Ƙuda da Kwaɗo
- Ɓarayin Rake
- Maraya
- Ɓarawon Gwal
- Tsiniyama da Lafiyana
- Yusufu da Bala
Wasanni
Karin Magana
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:
TweetLatsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin