Durbin Katsina

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Durɓi ta Kusheyi


Gabatawa

Durɓi gari ne a cikin jahar Katsina, wanda ke da tazarar kusan kilomita 32 daga birnin Katsina. Wannan gari shi ne asalin fadar masarautar Katsina. Akwai abubuwan tarihi a wannan gari da ke tabbatar da kasantuwarsa fadar mulkin Katsina ta farko.

Wannan gari yanzu an fi kiransa da Durɓi ta Kusheyi saboda samuwar kusheyi (ƙaburbura) irin na mutenen da. Wasu daga cikin ruwayoyin da muka samu na kunne ya girmi kaka sun labarta mana cewa kusheyin guda shida ne adadin sarakunan da suka zauna  a garin kafin komawar garin Katsina. Amma a wani ƙauli sun ce ba wai kusheyin sarakuna ba ne, a’a, kusheyi ne dai na jama’ar gari saboda a al’adar mutanen gurin idan mutum ya mutu akan binne shi da dukkan abubuwan da ya mallaka.

Wannan ra’ayi ya samu goyon bayan hukumar tarihi da al’adu ta Katsina (History and Culture Bureau), wanda wani jami’inta ya gaya mana cewa akwai wasu abubuwa da masana tarihiri suka haƙo wanda ke tabbatar da faruwar wancan zance, ita ma dai wannan maganar bata samu ƙarfafa da gani na zahiri game da shi abin da aka tono ɗin ba.

Daga cikin abubuwan tarihin da har yanzu ke raye a wannan gari akwai fadar masarautar wacce ke kewaye da duwatsu da suke a jere kamar Katanga da kuma sarƙin bishiyoyi. A cikin fadar a kwai wata kuka mai suna ‘Katsi’, wacce wasu ke alaƙanta samuwar sunan Katsina daga ita wannan kukar.


Fadar Sarakunan Farko ta Katsina da ke garin Durbi ta Kusheyi


Kukar Katsi

Sannan kuma akwai wani dutse mai ban al’ajabi da ake kira ‘Dutsen Bataretare’, dutsen da aka ce shi sarki Batare da jama’arsa suka bautawa. Majiyar kunne ya girmi kaka ta labarta mana cewa a wancan zamanin ana yiwa wannan dutse yanka, saboda haka idan mutum ya taka shi to zai haukace ko kuma ya mutu.


Dutsen Bataretare

Sannan kuma akwai kusheyin mutanen da, wato ƙaburbura, waɗanda daga su ne aka canjawa garin suna ya zama Durɓi ta Kusheyi.


Wani ƙabarin Mutananen Dauri (Kushewa)

Sannan kuma dai shi garin ya sha zama kushewa a kankansa, sai kuma daga baya mutane su sake komawa su zauna a cikinsa. A yanzu haka nan akwai jama’a a wannan gari.

Manazarta:


Ingawa T.L. (2006). Katsina a History of an Ancient City. Hamdala Prinitng and Publishing.

Lugga S.A. (2004). Katsina College. Lugga Press, Katsiana.

Mamman M. (2015). Tarihin Unguwannin Birnin Kastina. Ahmadu Bello Univeristy Press Ltd, Samaru, Zaria-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub