Katsina Kofar Kwaya

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙofar Ƙwaya, Katsina


Gabatarwa

Ƙofar Ƙwaya ƙofa ce da ke kan hanyar zuwa Dutsinma. Ta samu wannan suna nata ne daga sunan wani mai unguwa da ke zaune a unguwar da wannan ƙofa take. Sunan wannan mai unguwa shi ne ‘Magaji Ƙwaya’; Magaji Ƙwaya mutum ne jarumi (Ingawa, 2006). Amma a ruwayar Mamman (2015) ya kawo cewa sunan wannan ƙofa ya samo asali ne daga sunan wani basaraken Haɓe wanda ke mulkin wani gari mai suna Ƙwaya. Sannan kuma shi wannan basarake shi ke samowa sarkin wannan zamanin nasa hatsi, wato dawa da gero da sauransu. Sannan kuma ya ƙara da cewa wannan ƙofa ta ita ne wani waliyi mai suna Wali Joɗa ya fita garin Katsina lokacin da sarki ya kore shi.

Manazarta:


Ingawa T.L. (2006). Katsina a History of an Ancient City. Hamdala Prinitng and Publishing.

Lugga S.A. (2004). Katsina College. Lugga Press, Katsina

Mamman M. (2015). Tarihin Unguwannin Birnin Kastina. Ahmadu Bello Univeristy Press Ltd, Samaru, Zaria-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub