Katsina Kofar Marusa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙofar Marusa, Katsina


Gabatawa

Wannan ƙofa ta samo sunanta ne daga sunan wani mutum wanda ya shahara wajen kamun bayi, shi wannan mutum ‘Marusa’ ya ƙware sosai wajen kamun bayi, idan ya fita kamo bayi yakan cinnawa gari wuta sai jama’a su fita da gudu shi kuma ya kama na kamawa. A saboda wannan dalilin ne ma yasa ake yi masa kirari da Marusa mai wuta aljihu (Ingawa, 2006).

Bayan wannan kuma akwai wata ruyawar da ta tafi a kan cewa, sunan wannan ƙofa ya samo asali ne daga sunan wani basaraken garin Dutsi mai suna Usman Marusa, an ce duk lokacin da zai tafi ƙasarsa yakan fita ta wannan ƙofa haka nan ma idan ya tashi dawowa ta wannan ƙofa yake dawowa (Ingawa, 2006; Mamman, 2015).

Manazarta:


Ingawa T.L. (2006). Katsina a History of an Ancient City. Hamdala Prinitng and Publishing.

Lugga S.A. (2004). Katsina College. Lugga Press, Katsina

Mamman M. (2015). Tarihin Unguwannin Birnin Kastina. Ahmadu Bello Univeristy Press Ltd, Samaru, Zaria-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub