Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gwamnan Kano Muhammadu Abdullahi Wase 1993 - 1996



Kanal Abdullahi Wase

Gabatarwa

Kanal Muhammadu Abdullahi Wase shi ne gwamnan jahar Kano na goma sha biyu. Shi mutumin Wase ne ta cikin Jahar Filato. An haife a shekarar 1948 a garin Wase.

Karatu

Kanal Muhammadu Abdullahi Wase mutum ne mai kaifin ƙwaƙwalwa. Ya fara karatunsa na ƙaramar firamare (junior primary school) a garin Wase, bayan ya kammala kuma aka tura shi garin Pankshin inda ya yi karatunsa na babbar firmare (Senior Primary School) kamar yadda ake yi da. Daga nan kuma ya samu nasarar shiga Kwalejin Horas da Malamai (Toro Teachers College) da ke Toro. A nan ya fita da sakamakon jarabawa mafi kyau a dukkan faɗin Arewacin Najeriya.

Daga nan ya wuce zuwa Makarantar Tsaro ta Najeriya (Nigerian Defence Academy (NDA)) da ke Kaduna, a wannan makaranta ma shi ne ɗalibin da ya fi kowa ƙwazo a fannin kadet (Cadet). Ya kammala karatunsa a wannan makaranta ta (NDA) a shekarar 1970.

Kanal Muhammadu Abdullahi Wase ya samu nasarar fita ƙasashen waje dan yin kwasawasai. Daga cikin ƙasashen da ya je akwai Ghana, da kuma Birtaniya. Haka nan ma a Najeriya ya halarci kwas a makarantar sojoji ta Jaji.

Daga nan kuma ya samu zuwa jami’ar Pittsburgh, inda ya je ya samu digiri na biyu a fannin Mulki. A wannan makaranta ma sai da ya karɓi kyaututtukan da suka haɗa da kyautar ‘Donald Stone Award’ da kuma ƙungiyar tsofaffin ɗaliban jami’ar ita ma ta karrama shi. A dai wannan jami’a ta Pittsburgh ya sake canja fanni ya koma fannin injiniyarin ya sake yin digiri na biyu (M.Sc Transport Engineering and Management).

Gogayyar Aiki

Tun gama digirinsa na farko a makarantar soja (NDA) ta Kaduna, makarantar ta riƙe shi ta bashi aikin kwamanda (Officer Commanding Demonstration Company). Sannan kuma ya riƙe muƙamin darakta har zuwa shugaban hukumar zaɓen Nijeriya lokacin tana (NEC) wato (National Electoral Commision).

Zamowarsa Gwamnan Kano

Kanal Muhammadu Abdullahi Wase ya zamo gwamnan jahar Kanoa shekarar 1993, Muƙamin da ya riƙe har zuwa shekarar 1996.

Gudunmawarsa

Kanal Muhammadu Abdullahi Wase ya bayar da gudunmawa mai gwaɓi wajen ci gabanjahar Kano da haɓɓaka tattalin arziƙin jahar. Kusan babu wani ɓangare na jahar Kano da Kanal Wase bai taɓa ba. Imma dai kai tsaye ko kuma a fakaice, kamawa tun daga ɓangaren mulki, zuwa kasuwanci, lafiya, sufuri, walwala da jin daɗin jama’a, fannin noma, fannin ilimi da sauransu.

Ya faɗaɗa gidan gwamnatin jahar Kano, ya gina tituna arba’in a karkara, shi ya gina titin eastern by-pass, ya kawo motocin sufuri guda goma masu kujeru 39 sannan kuma ya bada kuɗin da yawansu ya kai Naira Miliyan 41.4 dan gina gurin gyara da sayo safaya fat.

Shi ya kafa bankin Dala (Dala Building Society), ya ƙarasa ginin masallaci da asibiti da ke sakatariyar Audu Baƙo, ya gina Wuman santa (Women Centre) da ke kan titin Zariya, ya gina magudanan ruwan da tsayinsu ya kai mita 575 da kuma wasu da tsayinsu ya kai mita 3000. Ya malala ayyukan da taskace su na da kamar wuya.

Manazarta:


Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Eɗecutive Governor, Government House, Kano.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ɗanyaro M.M. (1997). Kano State 30 Years of Statehood (1967 – 1997).

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Gwadabe M.M. (2008). Land, Labour and Taɗation in Kano Native Authority: the Case of Kumbotso District 1903-1953. History Department, Ahmadu Bello University, Zaria.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003.

Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.

Kano State Ministry of Commerce. (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Northern Nigerian Publishing Company Ltd. (1979). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Gaskiya Corporation, Zaria.

Obii-Mbta R.A. (1994). Alhaji Ado Bayero and the Rorayl Court of Kano. Carpricorn 25 Limited. Kano-Nigeria.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Coy, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub