Me ka ke nema?


Shafin Farko

Fesbuk



Babbar Helikwatar Fesbuk
Hoto daga:www.theonion.com


Gabatarwa

Fesbuk (Facebook), shafi ne na sada zumunta wanda wani matashin Ba-amurke mai suna Mark Zuckerberg ya ƙirƙira tare da haɗin guiwar abokan karatunsa a lokacin da suke karatu a Jami’ar Harvard ta ƙasar Amurka. Abokan nasa su ne Eduardo Saverin, Andrew McCollum, Dustin Moskovitz da kuma Chris Hughes.

Ita kuwa wannan Baturiyar kalma, wato Facebook, asalinta suna ne da aka haɗa daga sunaye guda biyu; face, wacce take da ma’ana ta fuska, da kuma book mai ma’ana ta littafi sai aka dunƙule su waje guda aka rubuta ta kamar yadda take wato Facebook aka kuma bata ma’ana ta littafin fuskoki. Shi kuma littafin fuskokin ya amsa cikakken sunansa a aikace da kuma yare, kasantuwar dama shi wani littafi ne da ake yi a jami’o’in Amurka wanda yake ɗauke da fuskokin ɗalibai wato hotunansu tare kuma da ƙarin wasu bayanai game da kowane ɗalibi domin samar musu da sauƙaƙƙiyar hanyar tuntuƙa.

Tun kafin shigar Mark Zukerbarg makaranta da shi da abokansa akwai wasu tsirarun jam’o’in Amurka da suka fara wallafa nasu littattafan fuskokin a kan Intanet domin amfanin ɗalibansu. Wannan fasaha ita Mark ya kwaikwaya, ya faɗaɗata tare kuma da ƙayata ta, kuma cikin iko da hikima ta Allah abu kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba wadda a yanzu da nake yin wannan rubutun duk faɗin duniya babu wani shafin sada zumunta da ya kai shi karɓuwa, yawan ma’aikata tare kuma da samar da kuɗaɗen shiga abin da ya mayar da shi matashin da ya fi kowane matashi kuɗi a duniya.

Wannan kuma saboda samun gamsuwa da masu amfani da shi suke yi a duniya saboda zamowarsa mai sauƙin aiki kuma kyauta. Wanda yake bai wa koma wane irin mutum ne damar yaɗa manufofinsa kyawawa ko akasin haka a faɗin duniya. Sannan kuma ana iya buɗe shi ta kwamfuta, wayar hannu, iPad, iPhone da sauran na’urorin shiga Intanet.


Fuskar Shafin Fesbuk

Tarihi

Tushen wannan fasaha da a yau biliyoyin mutane suke cin moriyarta a duniya shi ne wani shafin Intanet mai suna Facemash da shi Mark Zuckerbarg ya ƙirƙira a farkon ɗalibtarsa a wannan jami’a ta Harvard. Da farko ya saka hotunan wasu ‘yan makarantar tasu ne da ya samu daga shafin Facebook na ɗakuna tara da ke cikin jam’iar. Amma shafin bai ɗauki lokaci mai tsawo ba hukumar jami’ar ta tsinke shi daga Intanet.

A watan Janairun shekarar 2004, Mark Zuckerberg ya sake gina wani shafin Intanet ɗin mai suna The Facebook. Bayan ya samu nasarar kammala wannan aiki sai ya samu abokin karatunsa mai suna Eduardo Saverin suka zuba jarin Dalar Amurka dubu ɗai-ɗai suka yi wa shafin rijista mai adireshi “www.thefacebook.com”. Da aka ƙirƙiri shafin, sai aka taƙaita yin rijista a shafin ga iya ɗaliban Kwalejin Harvard. Amma sannu a hankali ya yaɗu zuwa wasu jami’oin da suke Columbia, Stanford da kuma Yale duk a cikin Amurka. Daga baya kuma sannu-a-hankali abu ya bunƙasa ya zama duk mai sama da shekaru 13 a duniya zai iya yin rijista.

Kamfanin ya buɗe ofishinsa na farko a cikin watan Yuli na shekarar 2004 a Palo Alto da ke California a Amurka. Sanan kuma ya canja suna daga “www.thefacebook.com” zuwa www.facebook.com kamar yadda yake a yanzu a cikin shekarar 2005.

Tun daga wancan lokaci zuwa yau, shafin yake hauhawa har ta kai ga a yau ɗin nan babu wani shafin sada zumunta da ya kai shi yawan masu amfani a duniya.


Taskira Asirin Mai Ɗaki a Fesbuk

Amfanin Fesbuk

Shafin Fesbuk shafi ne mai matuƙar amfani a wannan zamani da muke ciki. Shafi ne da ya sada zumunci a tsakanin dukkan na’ukan mutane ta fuskacin jinis, shekaru, ayyuka, sana’i'o, addinai da sauransu da suke sannan wannan duniya tamu. Saboda wannan dalili ne ma ya saka jama’a suke cikakken amfani da shi wajen yaɗa manufofinsu na siyasa, kasuwanci, addini da makamantansu. Kaɗan daga cikin ɗimbin amfanin Fesbuk akwai:

  1. Sadar da zumunci a tsakaknin ‘yan uwa, abokai, ƙawaye, abokan aiki da kuma sake ƙulla sabuwar dangantaka da wasu mutanen da a baya ba su san juna ba. Shiga nan ka sada zumunci da mutane Balangada.
  2. Kasuwanci: Fesbuk kafa ce mai tarin muhimmanci da ɗan kasuwa zai yi amfani da ita wajen bunƙasa harkarsa ta kasuwanci koma shi kansa Fesbuk ɗin ya zamar wa mai amfani kafar samun kuɗaɗen shiga. Ana gudanar da harkokin kasuwanci da dama da suka haɗa da tallata haja, sadarwa tsakanin abokan ciniki da sauran abubuwan da suka shafi kasuwanci masu tarin yawa. Idan kana son sanin yadda za ka tallata hajarka a Fesbuk latsa nan.
  3. Tattaunawa: Fesbuk yana bai wa mai amfani damar tattaunawa ta hanyar bidiyo da kuma rubutaccen saƙo wadda ka iya zama ta nan take ko kuma ta hanyar ajiye saƙo daga baya a gani a mayar da amsa. Wannan tattaunawar kuma tana iya zama ta ɗaiɗaikun mutane ko kuma a ƙungiyance. Latsa nan ka ga yadda ake yi.
  4. Saƙon Kar-ta-Kwana: Fesbuk yana bai wa mai amfani da shi damar aika saƙon kar-ta-kwana da ma kuma ajiye saƙon a duk lokacin da wanda aka turawa saƙon ya samu damar buɗe shafinsa zai ga dukkanin saƙoninsa ya karanta sannan kuma ya bayar da amsa. Latsa nan ka ga yadda ake tura saƙo da kuma karɓar saƙo a Fesbuk.
  5. Yaɗa Hotuna, bidiyo da kuma sauti. Latsa nan ka ga yadda ake yi.
  6. Neman Ilimi: Fesbuk kafa ce da za a iya amfani da ita wajen neman ilimi. Akwai shafuka da dama a wannan kafa ta Fesbuk da suke ɗura darrusan da mai amfani zai iya buɗewa ya karanta. Haka nan kuma ɗalibai za su iya buɗe zaure su riƙa tattaunawa game da darrusan da ake koya musu a makaranta domin samun ƙarin bayani da sauransu. Zaurukan Rumbun Ilimi, Taskira da Maidarasu duka misalai ne na irin zaurukan da mai amfani zai shiga domin samun ƙaruwar ilimi.
  7. Yaɗa Ilimi: Fesbuk kafa ce da za a iya amfani da ita wajen yaɗa ilimi. Misali, malamai za su iya buɗe zauruka domin bayar da darrusan kai tsaye ko kuma domin amfani baya. Latsa nan ka buɗe naka zauren ko kuma ka shiga nan ka buɗe naka shafin.


Fuskar Shafin Yaɗa Saƙonnin Rumbun Ilimi

Dukkan wata gajiya da za a iya samu tare da wannan shafi na sada zumunta mai suna Fesbuk, sai ka fara buɗe shafi naka na kanka da farko tukuna. Idan baka da shafin sai ka latsa nan domin sanin yadda za ka buɗe.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub