Shafin Farko

Alogirizim


Gabatarwa

Wannan kalma ta Algorithm ko kuma Algorithm ta samu sunanta ne daga sunan mashahurin malamin lissafin nan mai suna Abu Ja'afar Muhammad Ibn Musa al-Khawarizmi, kamar yadda ya zo a (Muhammad 2010, Wikipedia 2016, da Britannica 2010).

A fannin kimiyyar kwamfuta (computer science), Algorithm shi ne tsararrun matakan da kwamfuta za ta bi daki-daki domin ta aiwatar da wani aiki. Waɗannan matakai akan yi musu taswira (flowchart) domin a samu sauƙin aiwatar da su.

Ta wata fuskar kuma muna iya kallonsa a matsayin jere ko jadawalin ayyukan da za a yi wajen tsara softuwayar kwamfuta a bayyane filla-filla. Wato abun nufi shi ne cewa Algorithm yana iya zama cikakke, kuma gamsasshen, rubutattun abubuwan da za a yi domin tsara wata softuwaya da aikin da za ta yi tun daga shigar da bayanai har zuwa fitar da sakamako.

Karantar tsari da kuma dabarun tsara waɗannan matakai a fagen kimiyyar kwamfuta (Computer Science), shi ake kira Algorithm Design. Daga cikin abubuwan da ake koya a wannan fanni akwai: (sorting; search trees, heaps, and hashing; divide-and-conquer; dynamic programming; amortized analysis; graph algorithms; shortest paths; network flow; computational geometry; number-theoretic algorithms; polynomial and matrix calculations; caching; and parallel computing).

A fannin Lissafi kuma (mathematics), algorithm hanya ce ta warware sarƙaƙiyar lissafi ta hanyar dabarar maimaita matakai (steps) mafiya sauƙi. Sassauƙan misali shi ne yin doguwar rabawa.

Amfaninsa

Sarƙaƙiya da amfanin algorithm kullum ƙara faɗaɗuwa;a suke yi da faɗaɗuwar fannin kimiyyar kwamfuta (computer science), Saboda haka amfanin algorithm a wannan zamani da muke ciki yana da wahalar ƙayyadewa.

Manazarta:


Lund University. (2015). Algorithms. An ciro daga: http://cs.lth.se/english /algorithms/

Moshkovitz D. da Tidor T. (2012). Design and Analysis of Algorithms.

Massachusetts Institute of Technology. An ciro daga: http://ocw.mit.edu/courses/electrical-engineering-and-computer-science/6 -046j-design-and-analysis-of-algorithms-spring-2012/016). Ahmadu Bello. An ciro daga: https://en.wikipedia.org/wiki/