Abinci

Me ka ke nema?


Shafin Farko

AbinciGurasa

Gabatarwa

Wani abu mai matuƙar muhimmanci a rayuwar ɗan’adam shi ne abinci. Akan ci abinci ba domin yunwa ko jin daɗi ba. A’a, buƙatar abinci ta fi ƙarfin nan. Abinci wani abu ne da shi kaɗai ke baiwa jiki ƙarfi, da kariya tare kuma da haɓɓaka ƙwayoyin halittar jiki.

Ƙwayoyin halittun jikin ɗan’adam suna da yawa, kuma kowanensu yana da buƙatar wani nau’in sinadarin abinci domin ya bunƙasa sannan kuma ya zauna cikin ƙoshin lafiya. Abinci shi ne kaɗai zai iya yin wannan aikin.

Ma’anar Abinci

Abinci shi ne dukkan abin da za a ci sannan kuma ya baiwa jiki sinadaran da ya ke buƙata domin samun ƙarfi. Yawancin abincin da ake ci akan samo shi ne daga tsirrai da kuma dabbobi.

Kafofin Samun Abinci

Muhimman kafofin samu abinci ga ɗan’adam su ne tsirrai da kuma dabbobi. Nau'ukan tsirrai suna da yawa. Bincike ya tabbatar da cewa kusan nau'ukan tsirrai dubu biyu (2000) ake nomawa domin samun abinci. Wasu daga cikin waɗannan tsirrai sukan zama abinci dukkaninsu, wasu kuma wani sashensu. Sannan kuma sai dabbobi waɗanda suma mafiya yawansu sun dogara da tsirrai ne a matsayin nasu abincin.

Amfanin Abinci

Abinci yana bada gagarumar gudunmawa wajen tattalin lafiyar jiki da kuma bashi kariya daga kamuwa da cututtuka. Cin ingantaccen abinci mai gina jiki wanda ke ɗauke da sinadaran gina jiki, yana da matuƙar amfani.

A ra’ayin Suven (2016), ƙwayoyin halittar ɗan’adam (human cells), suna buƙatar nau’ukan sinadarin abinci 45, waɗanda aka kira jiga-jigai ko muhimman abinci, waɗanda dole a same su a cikin abinci mai inganci (abinci mai gina jiki). Biyu daga cikinsu ana samun su a cikin iskar shaƙa (oxygen) da kuma ruwa. Sauran 43 kuma, ana samun su a cikin nau’ukan sinadaran abinci guda 5 waɗanda suka haɗa da furotin (protein), maiƙo (fat), kabohaidiret (carbohydrate), mineral (minarals), da kuma bitamin (vitamin). Dukkan waɗannan sinadarai suna bada gudunmawa wajen aikin da jiki yake yi.

Su kuwa ƙungiyar abinci ta Amurka wato ‘Food and Agricultural Organization’ (FAO), cewa suka yi dole a samu abinci saboda jiki ya:

  1. Haɓɓaka, sannan ya sauya, sannan kuma ya gyara ƙwayoyin halitta na naman jiki (tissue);
  2. Ya samar da ƙarfi da kuma ɗumama jiki, don jikin ya samu damar yin tafiya da kuma yin aiki;
  3. Ya gudanar da ayyukan da suka shafi narkar da abinci a cikin jiki da sauransu;
  4. Ya kare jiki daga kamuwa da cututtuka sannan kuma ya warkar da jiki daga cututtuka, da sauransu.

Wata cibiyar kula da lafiya, wacce ke ƙasar Indiya mai suna ‘Health and Care’ cewa ta yi, abincin da muke ci shi ne kaɗai kafar da take samar da ƙarfi da gina jiki ga jikkunanmu (Health and Care, 2010).

Ita Kuwa Fantar (2016) cewa ta yi, aikin da abinci yake yi ya fi ƙarfin gamsar da buƙatar ɗanɗano ko yunwa. Abinci shi ke samar da sinadaran da jiki ke amfani da su don ya girma cikin ƙoshin lafiya.

Manazarta:


Fantar S. (2016). 5 Classification of Nutrients. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: www.healtheating.sfgate.com/

Food and Agricultural Organization (2005). Healthy and Balanced Nutrition is Important for Everyone. Food and Agricultural Organization of the United Nations. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.fao.org/docrep/005/y4168e05.htm

Health and Care (2010). Importance of healthy food and diet in our life. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: www.healthandcare.in/healthy -food_importance

Suven (2016). Importance of Food. Hub Pages Inc. an ciro a shekarar 2016, daga shafin: hubpages.com/health/importance-of-food

Wikipedia (2016). Food. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: htpps://en.wikipedia.org/wiki/food


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub