Shafin Farko

Amfanin Kwamfuta


Gabatarwa

Amfanin kwamfuta a yau wani abu ne da ke da wahalar ƙididdiguwa, saboda kusan babu wani ɓangare na rayuwa da kwamfuta ba ta shafa ba, kaɗan daga cikinsu su ne:

  1. Ilimantarwa: Kwamfuta wata babban makami ce ta samun ilimi wacce ke baiwa mai amfani damar zama tutur yana karatu da ita ba tare da ƙosawa ba. Ana samun wannan ta hanyar amfani da furogiram ɗin da aka shirya domin ilimantarwa misali, softuwayar Maidarasu wacce za ta baka damar koyon karatun alƙur’ani, littattaffai, sanin tarihi, koyon ibada dama sauran fannonin ilimin addinin Musulunci duka cikin harshen Hausa.

  2. Ɗalibai suna aiki da kwamfuta
    An ciro daga: www.schoolsworld.tv

  3. Nishaɗantarwa: Ana amfani da kwamfuta wajen samun nishaɗi, misali, kallon fim, sauraron waƙoƙi, d.s.
  4. Adana Bayanai: Ana amfani da kwamfuta wajen adana bayanai, wani babban muhimmanci da kwamfuta ke da shi a nan fiye da komai wajen adana bayanai shi ne bayar da bahasi nan take.

  5. Yanna kallon wasan-kwaikwayo a kwamfuta domin sanun nishaɗi.
    An ciro daga: www.patriyaasia.blogspot.com

  6. Nazari da Bincike: Ana amfani da kwafutoci wajen gudanar da nazari da bincike a kowane fanni na ilimi.
  7. Gwaje-Gwajen Kimiyya da Fasaha: Ana amfani da kwamfuta wajen gudanar da gwaje-gwajen kimiyya da fasaha don gano wasu abubuwa. Kamar gano ko akwai wani nau’in ma’adani a guri.
  8. Aune-Aunen Kimiyya: Ana amfani da kwamfuta a asibitoci don gwada jini, fitsari, d.s.


    Kwamfuta na kula da maras lafiya
    An ciro daga: www.heraldextra.com

  9. Sadarwa: Ana amfani da kwamfuta wajen sadarwa.
  10. Sana’o’i: Kwamfuta wata kafa ce da ta samar da guraben sana’a, wanda hatta matayen da ke cikin gidajensu na aure za su iya amfani da wannan dama wajen samun kuɗaɗen shiga.

Manazarta:


Tsangarwa A.M. (2010). Kwamfuta a Sauƙaƙe, Sabon Bugu. Tsangarwa ICT Limited, Kano-Nigeria.