Shafin Farko

HTML


Gabatarwa

Yare wata kafa ce ta sadarwa tsakanin halittu, masu rai da motsi da kuma ma marasa rai. Misali ana tattaunawa tsakanin mutum da mutum, tsakanin mutum da dabba, ko kuma tsakanin mutum da wata na’ura kamar kwamfuta ko wayar tafi-da- gidanka da sauransu ta hanyar yaren da mai magana da wanda ake magana da shi za su iya fahimta.

HTML yare ne da masaninsa ke iya magana da kwamfuta a fakaice ta hanyar web-burawuza (web-burawuza wacce ake rubuta ta da “Web browser” a Turance), ita wbe-burawuza softwaya ce da babban amfaninta shi ne buɗe shafukan Intanet sannan kuma ta baka dama ka yi yadda ka ke so da su kamar ajiyewa, buga su a takarda, turawa wani, da sauransu. Misalansu sun haɗa da: "Internet Explorer, Opera, Opera Mini, Mozilla Firefox da sauransu".

Ma’anar HTML

HTML taƙaitaƙawa ce da ke da ma’ana ta “Hypertext Markup Language”, wanda kuma shi ne gama-garin yaren kwamfuta da ake shiryawa tare da tsara shafukan Intanet (web pages) da shi. Wannan kusan shi ne ƙashin bayan fasahar da ake amfani da ita wajen tsara shafukan Intanet da suka haɗa da waɗanda ake amfani da su (wato ake buɗe su) ta kwamfuta, wayar hannu, aifad, da sauransu.

Tarihi

A cikin shekarar 1980 wani mutum masanin kimiyyar kwamfuta kuma ɗan asalin Birtaniya mai suna Timothy Berners-Lee shi ya ƙirƙiri wannan fasaha lokacin da yake wani kontiragi a cibiyar nazarin ‘Physics’ ta CERN da ke ƙasar Switzerland (Microsoft Encarta, 2009; Encyclopaedia Britannica, 2010; Wikipedia, 2016).

Muhimmancinsa

  1. Yana da sauƙin rubutawa.
  2. Yana da sauƙin ganewa, har ma mutum yakan koye shi da kansa.
  3. Kusan dukkan web-burawuzozi suna gane shi.
  4. Rashin nauyi: Bashi da nauyi dan haka web-burawuzozi suna saurin buɗe shafin da aka tsara da shi.
  5. Sauƙin sarrafawa: Ana iya sarrafa shi ta hanyoyi da dama. Misali za a iya cakuɗa shi da wasu yarurrukan kamar irin su CSS, Javascript, VB Script, da sauransu.
  6. Karɓar baƙi: kowane mutum yana iya aiki da shi, kamar a ce yara da manya, maza da mata, kowa yana iya aiki da shi.

Gazawarsa

  1. Sandararren (static) abu ne wanda ke buƙatar sabuntawa (up-date) ɗaya-bayan-ɗaya idan buƙatar hakan ta taso. Wato ba za a iya seta shi ya riƙa sabunta kansa-da-kansa kamar wasu daga cikin yarukan gina shafin Intanet ba.
  2. Yana sassaɓawa daga burawuza zuwa wata. Abin nufin idan aka buɗe shafin da aka yi da HTML a Internet Explorer, ana iya samun canjin launi da ma wasu abubuwan idan aka buɗe shi a wata burawuzar daban.
  3. Yana da ƙaranci damammakin tsara (styles) shafuka.

Amfaninsa

  1. Ana gina shafin Intanet da shi.
  2.  Ana tsara abubuwan wayar hannu da shi.
  3. Ana shirya faifan sidi da shi.

Manazarta:


HTML. (2010). Encyclopædia Britannica. Encyclopaedia Britannica Ultimate Reference Suite. Chicago: Encyclopædia Britannica. Raghupati. (2011).

Advantages of HTML. VTechSEO. An cirio daga: www. vtech-seo.com/web-design-articles/advantages-of-html.html

Storey P. A. (2009). Hypertext Markup Language (HTML). Microsoft® Student 2009 [DVD]. Redmond, WA: Microsoft Corporation, 2008.