Kunu
Gabatarwa
Abinci ne da ake samarwa daga gero. Yana ɗauke da sinadaran da ke taimaka wa jiki ya yi ƙwari.
Ire-Iren Kunu
Akwai nau’ukan kunu da Bashaushe yake yi a Ƙasar Hausa da dama. A wannan rubutun za mu magantu a kan:
- Kunun Tsamiya.
- Kunun Kanwa.
- Kunun Gyaɗa.
- Kunun Nono.
- Kunun Zaƙi.
Kunun Tsamiya
Sunan wannan kunu ya samo asali ne daga tsamiyar da ake jiƙawa a yi kunun da ita.
Kayan haɗi
- Gero.
- Tsamiya.
- Kayan Ƙamshi (Kananfari, masoro da sauransu).
- Za a surfa gero, a tankaɗe shi a ware dusa sannan a wanke shi a daka ko a niƙa.
- Sai a tankaɗe niƙaƙƙen garin gero a fitar da tsaki.
- A jiƙa tsamiya ta jiƙu a cikin mazubi mai tsafta.
- Sai a ɗebi garin kaɗan a jiƙa shi da ruwan sanyi tsararo abin da ake kira ruwan sirki.
- Sannan a sake ɗiban wani gari a dama shi da kauri a cura gaya (Ida ana buƙata).
- Sai kuma a ɗebi wani garin gwargwadon buƙata a dama ƙullin kunu da ruwan tsamiya.
Dusar Gero
Tsakin Gero
Ruwan Tsamiya
Ruwan Sirki
Curin Gaya
Garin Kunu
Ƙullin Kunu
- A ɗora ruwa a kan wuta. Idan ya fara yin ɗumi sai a jefa gayan nan su tafasa tare har gayan ya dahu (Yana kama da curin ɗanwake).
- Sai a kawo tafasasshen ruwan nan a zuba a kan ƙullin kunu da aka dama sannan a rufe shi a mazubi mai kyau a bashi lokaci kaɗan ya haɗa jikinsa.
- Daga nan sai a kawo wancan ruwan sirki ana zubawa ana gaurayawa har kunun nan ya haɗu tsaf.
Dafaffen Gayan Kunu
Damammen Kunun Tsamiya
Ya damu da gaya kunun tsamiya, sama gaya ƙasa gaya kunun tsamiya.
Kunun Gyaɗa
Kayan haɗi- Gero.
- Ɓararriyar Gyaɗa.
- Tsamiya.
- Kayan Ƙamshi (Kanafari, masoro da sauransu).
- Za a surfa gero, a tankaɗe shi a ware dusa sannan a wanke a daka ko a niƙa.
- Sai a tankaɗe shi a ware tsaki da kuma gari mai lashi adana garin a mazubi mai kyau.
- A soya gyaɗa farar suya a murje ta a bushe sannan a markaɗa ta ko a daka sannan a adana ta a mazubi mai kyau.
- Sai a zuba gayaɗar can a cikin ruwa idan dakawa aka yi, idan kuma markaɗe ce to dama da ruwanta ake markaɗa ta sannan a tace. A ware butaci daban ruwan kuma a adana shi a mazubi mai kyau.
- A jiƙa tsamiya a cikin mazubi mai kyau.
- A ɗebi garin gero a dama gaya.
Soyayyiyar Gyaɗar Kunu
- A tafasa ruwan gyaɗar can da aka tace, tafasa uku.
- Idan ruwan ya fara yin ɗumi, sai a zuba gaya a ciki su tafasa tare.
- A dama garin kunu da ruwan tsamiya.
- A jiƙa wani garin na sirki da ruwan tsamiya.
- Idan ruwa ya tafasa sai a sauke a zuba shi a cikin damammen ƙullin kunu sannan a rufe shi a jira kaɗan.
- A buɗe rufaffen gaurayen ƙullin kunu da tafasasshiyar gyaɗa sannan a kawo ruwan sirki a riƙa zubawa ana gaurayawa.
Soyayyiyar Gyaɗar Kunu Tana Tafasa a Kan Wuta
Idan har aiki ya yi daidai, za a ga kunu yana sheƙi sannan kuma ƙamshi yana tashi.
Kunun Kanwa
Kayan haɗi- Gero.
- Kanwa.
- Kayan Ƙamshi (Kanafari, masoro da sauransu).
- A surfa gero sannan a bushe shi a cire dusa a wanke a daka ko a niƙa.
- A gyara kanwa ta hanyar ciccire bunu da kuma tsakowawin da ke cikinta sannan a jiƙa.
- A ɗebi garin gero a dama a cura gaya.
Ruwan Kanwa
- A ɗora ruwa ya tafasa.
- Idan ruwa ya fara ɗumi sai a jefa gaya a ciki su tafasa tare.
- A dama ƙullin kunu da ruwan kanwa.
- A sauke tafasasshen ruwa a kwara a kan ƙullin kunu sannan a rufe na wasu ‘yan mintuna da basu wuce biyu ba zuwa uku kai har ma biyar ya danganta da yawan kunun.
- A buɗe kunu a gauraya har sai ya haɗa jikinsa.
Kunun Kanwa
Kunun Nono
Kayan haɗi- Gero.
- Nono.
- Kayan Ƙamshi (Ida nana buƙata)
- A surfa gero, a tankaɗe sannan a wanke a daka ko a niƙa.
- A dama ƙullin kunu da ruwan sanyi.
- A cura gayan kunu.
- A zuba nono a cikin mazubi mai kyau a adana.
Nono
- A ɗora ruwa ya tafasa.
- A jefa gaya a ciki su tafasa tare.
- A sauke tafasasshen ruwa a kurma a saman ƙullin kunu sannan a rufe zuwa lokaci kaɗan.
- A buɗe haɗin kunu a riƙa zuba nono ana juyawa har su haɗa jikinsu.
Dafaffen Kunu
Haɗaɗɗen Kunun Nono
Koko
Kayan haɗi- Gero.
- Kayan ƙamshi.
- A rairaye gero sannan a wanke ba tare da an surfa ba.
- A jiƙa wannan gero ya samu awanni 24 a ruwa. An fi so a jiƙa shi bayan sallar La’asar. Misali, daga 5:00 na yamma zuwa ta 5:00 ɗin yammar gobe.
- A fitar da gero daga cikin ruwan da ya kwana a wanke.
- A zuba kayan ƙamshi a ciki a markaɗa.
- A tace markaɗaɗɗen gero a fitar da butaci sannan a zuba shi a mazubi mai kyau a rufe shi zuwa safiya.
Gero da Kayan Yaji
Butacin Gero
- A tace garin gero da ya kwana a ruwa domin a samu gasara.
- A zubar da ruwan tsari (Ruwan da geron ya kwana a cikinsa).
- A ɗebi gasarar da ake da buƙata a dama ta a wani mazubin na daban a adana. Idan kuma tana da kauri sosai, sai a zuva ruwa a ɗan tsinka ta kaɗan.
- A sake ɗibar wata gasar mai ɗan kauri a dama gaya da ita.
- A dama ruwan sirki. Gasara ce ake dama ta tsararo da ruwan sanyi.
Kwanannen Ruwan Tsari Kafin a Tace
Ana Tace Ruwan Tsari Domin a Samu Gasarar Koko
Zallar Ruwan Tsarin Koko
Gasarar Koko
- A ɗora ruwa a tukunya ya tafasa.
- A zuba gaya a cikin ruwa idan ya fara ɗumi su tafasa tare.
- A sauke tafasasshen ruwa a zuba a cikin damammiyar gasarar koko sannan a rufe a jira na ɗan ƙaramin lokaci.
- A buɗe koko a riƙa zuba ruwan sirki ana gaurayawa har su haɗe jikinsu.
Kammalallen Koko
Idan gasara ta saura sai a sake zuba mata sabon ruwa a adana zuwa gobe.
Kunun Zaƙi
Kayan haɗiGero da kayan ƙamshi da sukari
Yadda ake yi- A surfa gero a wanke fes.
- A zuɓa kayan ƙamshi a cikin gero a markaɗa.
- A tace butacin gero daga cikin markaɗe.
- Sai a kawo ruwa a zuba bakin gwargwado.
- A zuba sukari gwargwadon baƙata.
Abinci
Ɗakin Karatu
Harshen Turanci
Jama'iyyun Siyasa
Kimiyyar Kwamfuta
.jpg)
Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin