Daura Ƙofar Sarki Bashar
Shafin Farko

Ƙofar Sarki Bashar


Wannan ƙofa ta ci sunanta na Ƙofar Sarki Bashar ne bayan wata ‘yar taƙaddama da aka samu tsakanin shi Sarki Bashar da gwamnati, wanda hakan ya jawo aka ɗan dakatar da shi daga karagar mulki. da hakan ta faru shi Sarki Bashar sai ya fita daga gidan sarauta ya ɗan tare a gonarsa. Da wannan tangarɗa ta gushe aka maida shi kan karagar Mulkin Daura, da zai koma sai ya shiga ta wannan ƙofa. Saboda wannan dalili sai ya sa aka riƙa kiran wannan ƙofa da suna Ƙofar Sarki Bashar. An samo wannan labari daga ofishin Wakilin Tarihi na Masarautar Daura a ranar 24 ga watan Mayu na shekarar 2016.

Manazarta:


Abubakar M.S. (2007). Taƙaitaccen Tarihin Daura. Majalisar Sarkin Daura. An buga a: Ammani Printing Press.

Tattaunawa da Wakilin Tarihin na Daura da kuma Dogarin Sarkin Daura mai suna Ɗandaushe, a ranar 24 ga watan Mayu na shekarar 2016.

Babban Shafin Tarihi
Masarautr Daura

Sarakunan Daura


Ƙofofin Daura


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub