Farfesa Wirth

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Farfesa Wirth



Hoto: www.compu terhistory.org Farfesa Wirth

Gabatarwa

Farfesa Wirth,  mutumin ƙasar Siwizlan (Switzerland) ne. Shi riƙaƙƙen furogirama ne (Programmer) kuma farfesa a jami’ar Fasaha ta Swiss (Swiss Federal Institute of Technology (ETH)) makarantar da a nan ya yi digirinsa na farko. Ya rubuta littattafai sannan kuma ya ƙirƙiri softwaya, ya kaɓi kyautar ACM.

Wannan takarda za ta ɗan tsakuro tarihinsa dan wallafawa a wannan ɗaki na karatu. Rubutun zai fuskanci haihuwarsa, karatunsa da kuma kaɗan daga cikin irin abubuwan da ya samar.

Haihuwarsa

Farfesa Wirth, haifaffen garin Winterthur na cikin ƙasar Switzerland. An haife shi a ranar 15 ga watan Fabarairu (February) na shekarar 1934, duba (Association of Computing Machinery, 2012; Hosch, 2016; Computer History Museum, 2016). Cikakken sunansa shi ne Niklaus Emith Wirth kamar yadda ya zo a (Hosch, 2016).

Karatunsa

Farfesa Wirth ya yi digirin Farko a jami’ar Swiss (Swiss Federal Institute of Technology) a fannin laturonik Injiniyarin (Electronic Engineering) a cikin shekarar 1959. Sannan ya yi digiri na biyu duk a fannin Laturonik Injiniyarin (Electronic Engineering) a jami’ar  Labal (Laɓal Uniɓersity), a birnin Quebec a cikin shekarar 1960. Daga nan sai Wirth ya tafi ƙasar Amurka  inda ya samu Digirin Digirgir, wato digiri na uku a fannin kimiyyar kwamfuta (computer science) a jami’ar Califonia (University of California) da ke Berkeley a shekarar 1963. Daga nan kuma sai ya wuce jami’ar Stanford (Stanford University)  inda ya samu muƙamisan na farfesa daga shekara 1963 zuwa 1967.

Gudunmawarsa

Bayan zamowarsa farfesa a Amurka, sai ya koma gida kuma tsohuwar makarantarsa gurin da ya karɓi digirinsa na farko ya ci gaba da karantarwa. Wirth, ya ƙirƙiri sashen karatun kimiyyar kwamfuta (computer science department) a wannan makaranta. A yunƙurinsa na samu wata kafa ta karantar da ɗalibai yadda ake shirya softwaya; wato furogiramin (programming), sai ya ƙirƙiri wani yaren shirya softwayar kwamfuta mai suna PASCAL a shekarar 1968 aka kuma fara amfani da shi a shekarar 1970. Wannan softwaya tana matuƙar bayar da gudunmawa a ɓangaren abin da ya shafi koyar da shirya softwayar kwamfuta (computer programming) a fannin karantarwa. Bayan wannan ma kuma ya ƙirƙiri wasu softwayoyin da suka haɗa da: EULER, ALGOL-W, da kuma MODULA.

Ƙarin a kan waɗannan yarurruka da ya ƙirƙira, ya kuma jagoranci ƙirƙirar Jigon softwaya (operating systems) da aka yi a Jami’arsa ta ETH. Wannan kalma ta ETH ita ce taƙaitacciyar kalmar da ake amfani da ita wajen faɗin sunan jami’arsa ta (Swiss Federal Institute of Technology). Waɗannan jigon softwaya su ne “Lilith da kuma Oberon operating systems”.

Farfesa Wirth ya bada muhimmiyar gudunmawa wajen ƙirƙira da kuma yaɗa ilimin kimiyyar kwamfuta (computer science). Farfesa ya rubuta littattafai a wannan fannin na kimiyyar kwamfuta (computer science) da suka haɗa da:

  1. Algorithms Plus Data Structures Equals Programs (Prentice-Hall series in automatic computation). Published 1975 — 8 editions.
  2. Compiler Construction, with Disk. Published 1977 — 3 editions.
  3. Project Oberon: The Design of an Operating System and Compilers. Published 1992 — 2 editions.
  4. Pascal User Manual and Report. Published 1974 — 8 editions.
  5. Algorithms & Data Structures. Published 1983 — 7 editions.
  6. Systematic Programming: An Introduction. Published 1972 — 4 edition.
  7. Programming in Modula-2 (Teɗts and Monographs in Computer Science). Published 1985 — 10 editions.
  8. Programming in Oberon: Steps Beyond PASCAL and Modula. Published 1992. Pascal User Manual and Report: ISO Pascal Standard. Published 1991 — 2 editions.
  9. Programming in Modula-2. Published 1982 — 5 editions.
  10.  Grundlagen Und Techniken Des Compilerbaus. Published 1996 — 6 editions.
  11. Compilerbau. Published 1984.
  12.  Pascal User Manual and Report: Reɓised for the ISO Pascal Standard. Published 1985.
  13. The Future of Software Engineering: Panel Discussions. Published 2011 — 2 editions.
  14.  Digital Circuit Design for Computer Science Students: An Introductory Teɗtbook. Published 1995 — 3 editions.
  15.  Principi di programmazione strutturata. Published 1990.
  16.  Algorithmen Und Datenstrukturen Mit Modula 2. Published 1989 — 2 editions.
  17.  Algorithms and Data Structures.

Kyaututtukan Yabo/Girmamawa (Awards)

Farfesa ya karɓi kyautar yabo ta “Turing Award” daga “Association of Computing Machine (ACM)”, a shekarar 1984. Sannan ya karɓi kyautar “IEEE Computer Pioneer Award” a shekarar 1988, sannan ya karɓi kyautar “IBM Europe Science and Technology Prize”, a shekarar 1988. Da sauran kyaututtuka da muƙaman girmamawa da ya samu.

Farfesa Wirth ya yi ritaya daga aikin koyarwa a cikin shekarar 1999.

Manazarta:


Association of Computing Machine. (2012). Niklaus E. Wirth A.M. Turing Award Winner. An Ciro Daga: http://amturing.acm.org/award_win ners/wirth_1025774.cfm

Brainy Quote (2016). Niklaus Wirth Quotes. An Ciro daga: http://www.brainy ƙuote.com/ƙuotes/authors/n/niklaus_wirth.html

Computer History Museum (2016). Niklaus Wirth. An ciro daga: http://www. computerhistory.org/fellowawards/hall/bios/Niklaus, Wirth/

Hosch W.L (2016). Niklaus Emil Wirth Swiss Computer Scientist. Encylopaedia Britannica Inc. An ciro daga: http://www.britannica.com/biography/


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub