Bukukuwa da Wasanni

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Bukukuwa da Wasanni


Gabatarwa

Biki taro ne da ake yi a Ƙasar Hausa domin taya juna, ko wani, ko wasu murna wanda ake gudanar da shi a nishanɗance ta hanyar kaɗe-kaɗe, raye-raye, waƙe-waƙe, tanɗe-tanɗe, da lashe-lashe.

Kenan, duk wani taro da ya haɗe waɗannan abubuwa guda huɗu ko wasu daga ciki, to kai tsaye za a iya kiransa da biki.

Akwai bukukuwa da dama da ake gudanarwa a Ƙasar Hausa. Amma waɗanda aka fi sani su ne; bikin aure, bikin suna, bukukuwan salla, bikin mauludi, bikin takutaha, bikin kalankuwa, da sauransu. Bukukuwa a Ƙasar Hausa sun kasu gida biyu. Farfesa Ɗangambo (1984), ya ce, akwai bukukuwan da suka shafi addini, da kuma bukukuwan da ba su shafi addini ba.

Bukuwan da suka shafi addini

Waɗannan bukukuwa su ne bukukuwan da ake yi a lokutan da ake gudanar da wata hidima ta addini. Daga cikin irin waɗannan bukukuwa akwai bikin salla ƙarama da salla babba, bikin mauludi, bikin takutaha, bikin maukibi, bikin sallar gani, bikin walima, da sauransu.

Bukukuwan da basu shafi addini ba

Waɗannan su ne bukukuwn gargarjiya na Bahaushe waɗanda suka haɗa da bikin aure, bikin suna, bikin shan kabewa, bikin naɗin sarauta, bikin hawan daba, bikin kaciya da sauransu.

Nau'ukan Bukukuwa

  1. Bikin Sallah
  2. Bikin Hawan Daba
  3. Wasan Dambe
  4. Wasan Shaɗi
  5. Wasan Kokawa

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Darrusan Hausa

  • Darrusan Hausa

  • Bukukuwa


    Wasanni



    Ƙasar Hausa



    Musulunci


    Zuwan Turawa


    Tarbiyya


    Kayan Kiɗan Hausa


    Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


    Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



    Sauran Shafukanmu:

    Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub