Kayan Busa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kayan Busa


Su ne waɗanda ake fura iska da baki ta fito ta cikinsu tare kuma da sarrafa iskar da hannu a lokacin da ake furawa da baki domin samar da amon da ake so. Ga wasu daga cikin kayan busar Hausawa: Algaita, farai, sarewa, kakaki, ƙaho, kobiris, kusumburwa, zilli, liƙo/siriki, turta da sauransu.

Sassan Jikin Kayan Busa

Kayan busa abubuwa ne da suka bambanta da juna, kusan kowane ɗayansu ya bambanta da saura. Amma ba ka rasa kowane da waɗannan abubuwa uku:

  1. Gangar jiki: Ita ce gundarin sashen abin busa, ta fi kowane sashe girma. Ita ce asalain abin da ke fitar da siffar kayan busa, kuma tana bambanta da bambancin abin da aka yi ta da shi.
  2. Baki: Shi ne gurbi ko sashen da ake busa abin busa da shi. Wasu bakunan dasa su ake yi kamar bakin algaita, wasu kuma  ƙofa ce ko tsaga da ake yi a jikinsu kamar bakin ƙaho ko liƙo da sauransu.
  3. Ƙofa: Ƙofa a nan na nufin mazurarar amo, wato kafar da amon muryar abin busa take fita.

Manazarta:


Gusau S.M. (2017). Kayan Kiɗan Hausa. Centuary Research and Publications, Kano – Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.  

Tattaunawa da Umaru mai gurmi a garin Uke ta jahar Nassarawa a ranar Alhamis 14/3/2018.

Tattaunawa da Sarkin Kiɗan garin Alitini, Isma'ila Namarke, a garin Alitini, ƙaramar hukumar Warawa, a Jahar Kano, Najeriya. A ranar 17 ga watan 6, na shekarar 2017.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub