Tatsuniya: Gizo da Saniya

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tatsuniya: Gizo da Saniya


Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

A wani gari, an yi wata Saniya mai ciki. Wata rana wannan saniya tana cikin shan ruwa a rafi, sai ta haifi ‘ya’ya guda huɗu, uku daga cikinsu mata ne, ɗaya kuma namiji. Bayan da ta gama shan ruwanta, sai ta fito da ‘ya’ya matan nan guda uku, ɗayan kuma wanda shi ne namiji, sai ta bar shi a cikin ruwan.

Bayan ta fito da su daga ruwan nan sai ta samu guri ta ɓoye su, ita kuma ta tafi kiwo. Da ta je kiwo ta samu abinci ta ci, ta kuma kawo wa ‘ya’yan nata.  Da ta iso bakin rafin nan sai ta rera waƙa tana kiran ‘ya’yan nata, tana cewa:

Sari’atul-ma zo ki ci, mazariƙi-mazandamu ma zo ki ci, maza-dandama ma zo ki ci, amma kai na cikin ruwa ban da kai.

Shi ke nan da ‘ya’yan saniyar nan suka ji haka sai suka fito suka ci abincin nan suka sha ruwa, suka kwanta. Ita kuma saniyar nan sai ta sake barin ‘ya’yan nan nata ta tafi kiwo. Da ta je, sai ta ci ta ƙoshi, sannan ta ɗebo wa ‘ya’yanta. Da ta zo sai ta sake cewa:

Sari’atul-ma zo ki ci, mazariƙi-mazandamu ma zo ki ci, maza-dandama ma zo ki ci, amma kai na cikin ruwa ban da kai.

Da ‘ya’yan saniyar nan suka ji, sai suka fito, suka ci abinci suka sha ruwa, suka kwanta. Ashe Gizo yana laɓe yana ganin abin da ke faruwa. Ai kuwa saniyar nan na tafiya, sai Gizo ya fito, ya kama rera waƙa. ‘Ya’yan saniyar nan suna ji, amma suka ƙi fitowa saboda Gizo ba daidai yake waƙar ba. Da Gizo ya ga sun ƙi fitowa, sai ya tafi ya sake laɓewa.

Can bayan wani lokaci sai ga saniya ta sake dawowa. Tana zuwa sai ta kama rera waƙa kamar yadda ta saba yi:

Sari’atul-ma zo ki ci, mazariƙi-mazandamu ma zo ki ci, maza-dandama ma zo ki ci, amma kai na cikin ruwa ban da kai.

Da ‘ya’yan saniya suka ji ita ce, sai suka fito suka ci abinci sannan suka sha ruwa suka sake komawa suka ɓoye. Ita kuma saniya ta sake tafiya kiwo.

Bayan tafiyar Saniya ba da jimawa ba, sai Gizo ya sake fitowa. To, yanzu Gizo ya haddace abin da saniyar nan take faɗa, saboda haka yana rera waƙar nan, sai ‘ya’yan saniyar nan suka fito. Suna fitowa sai Gizo ya kama su ya gudu da su, ya cinye.

Can bayan wani lokaci sai saniya ta dawo daga kiwo da abincin ‘ya’yanta guda uku. Da ta zo, ta yi waƙa, ta yi waƙa, ta yi waƙa, amma shiru ba ta ga kowa ba. Can sai ta juya ta ce: To kai na cikin ruwa zo ka ci. Shi kuma sai ya ce, “Ni na cikin ruwa ba ni ci, alherin Allah ya ishen”. Da Saniya ta ji haka sai kawai ta faɗi ta mutu.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub