Tatsuniya: Kuturu, Makaho da Kurma

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tatsuniya: Kuturu, Makaho da Kurma


Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Wata rana kuturu da kamaho da kurma suka ce za su je satar yalo. Da suka je gonar sai makaho da kuturu suka kasa cirowa, sai kurma ya yi ta cira yana ci, sai makaho da kuturu suka ce da shi idan bai ciro musu ba za su fallasa su. Sai ya ce ba zai ciro musu ba. Sai suka ƙwalla ihu a gonar suka ce ga mu nan muna satar yalo. Sai aka biyo su da gudu. Suna cikin gudu sai kurma ya taka ƙaya, sai ya ci gaba da gudu yana cewa “na mama aya”. Da suka iso gida sai suka cire masa ƙayar, da suka cire masa sai suka huta. Bayan sun huta sai suka ci abinci.

Washegari, sai suka ce a zo a je satar rake. Da suka je gonar rake sai kuturu da kurma suka ɗebi rake suka gudu suka bar makaho a gonar, sai suka hau kan bishiya suna sha. Sai shima makaho ya ɓallo ya gudu, da ya gudu sai ya yi ihu ya ce ga su nan suna satar rake.

A garin saukowa daga sama sai kurma ya sauko ya bar kuturu a sama aka kama shi aka dake shi. Kurma da makaho kuma suka je gida. Can daga baya sai kuturu ya zo, sai aka tambaye shi me ya sa bai dawo da wuri ba, sai ya ce kama shi aka yi aka dake shi, sai suka ce a zo a koma sai kuturu ya ce shi ba zai je ba.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub