Karin Magana I

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Karin Magana I


  1. A juri kai ruwa rafi, wata rana gora zai fashe.
  2. A kai gwauro, a kai mari.
  3. A saka a baka, ya fi a rataya.
  4. A tambayi kaza hanyar rafi? A tambayi agwagwa a sha labari.
  5. Abokin kuka, ba a ɓoye masa mutuwa.
  6. Alamar ƙarfi, tana ga mai ƙiba.
  7. Albasa, bata yi halin ruwa ba.
  8. Allah ya tsari gatari, da saran shuka.
  9. An yi ba a yi ba, rufin ƙofa da ɓarawo.
  10. An yi ba a yi ba, shuka a idon makwarwa.
  11. Ana zaton wuta a maƙera, sai ta tashi a masaƙa.
  12. Ba a yi ciki dan tuwo kawai ba.
  13. Ba da ni ba, gaɗa a hurumi.
  14. Ba girin-girin ba, ta yi mai.
  15. Baki da gashin wance, ba kya yi kitson wance ba.
  16. Bakinka, ya tsuliyarka.
  17. Bishiyar giginya, na nesa ka sha inuwarki.
  18. Ciki da gaskiya, wuƙa bata huda shi.
  19. Ciwon 'ya mace na 'ya mace ne.
  20. Da rarrafe, yaro kan tashi.
  21. Da rashin kira, Karen bebe ya ɓata.
  22. Da rashin tayi, akan bar araha.
  23. Da walakin, goro a miya.
  24. Daki-bari.
  25. Dare, mahutar bawa.
  26. Duk girman ɗantsako, ƙwai ya fi shi.
  27. Duk wanda ya daka rawar wani, zai rasa turmin daka tasa.
  28. Duk wanda ya ƙona rumbunsa, ya san inda toka take tsada.
  29. Fallasa, auren bashi.
  30. Faɗan gwaggo a kofa.
  31. Ga maciji ana bin ja.
  32. Gani, ya kori ji.
  33. Gaskiya ɗaci gareta.
  34. Gutun gatarinka, ya fi sari ka bani.
  35. Haihuwa ɗaya, horon gindi.
  36. Hauka da naɗe-naɗe, ɗanwake ya ga tubani.
  37. Idan ana ta ɓarawo, to a yi ta mabi sawu.
  38. Idan ka ga tsohuwa tana rawa a kasuwa, to ta daɗe tana yi.
  39. Idan ka je gari ka kowa da jela, kai ma nemi ka ɗaura.
  40. Idan kunne ya ji, jiki ya tsira.
  41. Idan makaho ya ce a yi wasan jifa, to ya taka dutse.
  42. Ina raba ka da yin kiwo, kana kyalla ta haihu.
  43. Idan ɓera da sata, to daddawa ma da wari.
  44. Ihunka na jiyo.
  45. Jiki, bai fi jiki ba.
  46. Jiki, magayi.
  47. Kafin ka ga biri, biri ya ganka.
  48. Kai ka faɗa? Uwar sarki a kan doki.
  49. Kamar da gaske, karuwa ta ga noman ɗankoli.
  50. Kar kaza ta tono wuƙar yanka ta.
  51. Komai nisan dare, gari zai waye.
  52. Komai nisan jifa, ƙasa zai faɗo.
  53. Kowa ya ci zomo, ya ci gudu.
  54. Kowa ya ga balbela, da farinta ya ganta.
  55. Kowane tsuntsu, kukan gidansu yake yi.
  56. Kura, ta san gidan mai babban sanda.
  57. Lumbu-lumbu, wutar ƙaiƙayi.
  58. Mahaukaciyar kasuwa, sa gabanki inda ki ke so.
  59. Mai guri ya zo, mai tabarma ya naɗe.
  60. Mai haƙuri, yakan dafa dutse ya sha romonsa.
  61. Mai ɗaki, shi ya san inda yake yi masa yoyo.
  62. Marena kaɗan, zai haƙura da babu.
  63. Matar mutum, ƙabarinsa.
  64. Matar shige bata daraja.
  65. Mu gani a ƙasa, an ce da kare ana biki a gidan su kura.
  66. Murucin kan hanya/dutse, baka fito ba sai da ka shirya.
  67. Na shiga ban ɗauka ba, bata fidda ɓarawo.
  68. Nesa, ta zo kusa.
  69. Ni ya kai, kai ya ni.
  70. Ƙarya fure take, bata 'ya'ya.
  71. Ƙofar Allah, ta fi ta cali.
  72. Ƙwai a baka, ya fi kaza a akurki.
  73. Ramin ƙarya, ƙurarre ne.
  74. Rana bata ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya.
  75. Rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya.
  76. Ranar wanka, ba a ɓoyon cibi.
  77. Ruwa, ba sa'an Kwando ba ne.
  78. Ruwa, baya tsami banza.
  79. Sa toka sa katsi.
  80. Sabon shiga, ɓarawo da sallama.
  81. Sai bango ya tsage, ƙadangare yake samun wajen shiga.
  82. Saki reshe, kama ganye.
  83. Sammakon bubuƙuwa.
  84. Samun duniyar ɗantsako.
  85. Samun na sameka.
  86. Sannu-sannu bata hana zuwa, sai dai a daɗe ba a je ba.
  87. Sara da sassaƙa, basa hana ganji toho.
  88. Shiru-shiru ba tsoro ba ne gudun magana ne.
  89. Talaka baya tashin talaka, sai tashin talaka ya zo.
  90. Tsautsayin takaba. auren shiɗaɗɗe.
  91. Tsuntsu, duka tsuntsu ne.
  92. Tura, ta kai bango.
  93. Wanda bai ji bari ba, zai ji hoho.
  94. Wane kare ne ba bare ba?
  95. Wayo, ya san na ƙi.
  96. Wayon a ci, an kori kare daga gindin ɗinya.
  97. Yaro bari murna, karenka ya kama zaki.
  98. Yaya gara takan yi da dutse? Sai kallo.
  99. Zakaran da Allah ya nufa da cara, ana muzuru ana shaho sai ya yi.

BayaKarin Magana   Gaba Karin Magana II


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub