Tatsuniya: Kura da Kare

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tatsuniya: Kura da Kare


Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Akwai wani mafarauci ana ce da shi Fautaranga, sai wata rana ya je gidan namun daji (dabbobin daji) ya ce da wa za mu farauta? Sai kura ta ce ni, sai ya ce da ita “dama ke nake nema”, sai suka tafi tare da kura. Suna cikin tafiya sai kura ta ce da shi tana jin yunwa, sai ya ce da ita ta bari sai sun ƙara gaba zai bata abinci.

Suna cikin tafiya sai suka isa wani kogi, sai ya ce da ita ta sha ruwa iya shanta. Da ta sha ta ƙoshi, sai shi kuma ya kafa bakinsa ya shanye dukkan ruwan kogin. Bayan ya shanye sai suka ɗebo kifayen cikin kogin suka cinye. Suna nan har dare ya yi, saboda haka da za su kwanta barci sai Fautaranga ya ce da kura “kar ki kwanta a bayana ina tusar ƙashi” sai kura ta ce bata yarda ba sai ta kwanta. Suna kwance can cikin dare sai kura ta ji ƙashi ya zo ya cake ta ya koma, sai ta tashi ta koma gabansa ta kwanta, da ta kwanta sai da gari ya waye sai kura ta ce da shi ashe dama abin da ka faɗa gaskiya ne ba ƙarya ba?

Daga nan sai ya ce da kura yanzu za mu je wajen wasu giwaye guda goma, idan mun je ki zage su, idan suka biyo ki sai ki yi tsalle ki faɗa cikin cikina. Da suka je sai kura ta zagi giwayen nan, da suka biyo ta da gudu sai ta yi tsalle ta faɗa cikin Fautaranga. Shi kuma sai ya kama giwayen nan ɗaya-bayan-ɗaya ya yayyanka su.

Kura kuma daga cikin maharbin nan sai ta wuce hancinsa ta taras da kasuwa tana ci a ciki, a cikin kasuwar sai ta je gurin mai tsire ta ce da shi za ta yi masa talla, sai ya ɗora mata tallar a faranti. Can sai Fautaranga ya kira kura ya ce “kura”, ya ji shiru, ya sake cewa “kura”, ya ji shiru, sai ya fyato ta (kamar yadda ake fyace majina) da farantin talla a kanta, da ya ga haka sai ya ce da kura ta je ta mayar da faranti ta fito su tafi.

Sai kura ta mayar da farantin, shi kuma mai tsire ya bata tsire ladar talla, da kura ta karɓa sai ta zauna ta cinye tsiren, bayan ta cinye sai ta fito suka ƙara gaba.

Da za su tafi sai aka ɗorawa kura cinyar giwa ta kasa tafiya, sai ya ɗauka ya raba shi kashi uku ya ɗora mata kaso ɗaya, shi kuma ya ɗauki dukkan sauran. Daga nan sai suka tafi gida.

Da suka iso gida sai ya bata kasonta ya ce ta je ta soya ta ci. Da ta soya ta ji daɗi, sai ta kira kare ta ce su zo su koma farautar, sai ta je aka haɗa mata hancin laka. Suna cikin tafiya sai kare ya ga zomo, da ya ga zomon sai ya ce da kura in ɗauka? Sai kura ta yi masa shiru, shi kuma sai ya faki idonta ya ɗauka ya jefa a ruzu.

Bayan sun yi doguwar tafiya, sai kare ya ce da kura yana jin ƙishirwa, sai suka je kogin da suka sha ruwa da Fautaranga, sai kura ta ce da kare ya sha iya shansa, kare ya sha, daga nan sai kura ta kafa kanta ta kasa shanye ruwan wannan kogi, da ta kasa sai kare ya ce da ita ya kika kasa shanyewa? Sai ta ce ai yanzu bana jin ƙishirwa. Sai kura ta ce da kare su shiga su kamo kifi, bayan da suka samu ɗan abin da suka samu, sai kura ta ce su ci gaba. Suna cikin daji dare ya yi musu, sai kura ta ce da kare “kar ka kwanta a bayana ina tusar ƙashi”, sai kare ya kwanta, har gari ya waye kura bata yi tusa ba. Sai kare ya tambayeta ya aka yi baki yi tusar ƙashin ba? Sai kura ta ce ai yau bata ci abinci ba shi ya saka. Daga nan sai ta ce da shi za su je wajen wasu giwaye, idan sun je kare ya tsokano giwayen nan idan sun biyo shi ya yi tsalle ya faɗa cikin hancinta.

Da suka isa sai kare ya tsokani giwaye, da suka biyo shi sai ya yi tsalle ya dira a kan hancin kura (hancin taɓo), sai hancin ya ruguje, daga nan sai kura ta ce kowa ya yi ta kansa, ka bi ta tudu na bi ta gangare. Da suka iso gida sai kura ta je gurin Fautaranga ta gaya masa cewa sun je wajen giwayen nan amma sun biyo su da gudu. Sai ya ce da ita, me ya hana ki zuwa ki karɓi magani a wajena kafin ku tafi?

Daga nan sai kare da kura kowa ya kama gabansa, da suka isa gidajensu sai kare ya ɗauko zomon nan ya fara suya, da kura ta ji ƙanshi sai ta laɓaɓo gidan kare ta taras da shi yana suya. Sai kura ta tambaye shi ta ce “kai kuma wa ya baka nama ka ke soyawa?” Sai kare ya ce da ita suya aka bashi idan ya gama ya suɗe kaskon. Sai ta ce da shi tana son naman idan kuma ya hanata ta cinye shi duka shi da naman. Sai ta ce za ta je ta dawo kafin ya gama.

Fitar kura ke da wuya sai kare ya je ya ɓoye naman nan a ɗaki, sai ya suɗe kaskon ya tofa yawu da majina a ciki, ya soya, ya ajiye. Da kura ta dawo sai ya bata sai ta suɗe, sai ta ce “kare wannan naman da daɗi idan aka baka zaka bani?” Sai ya amsa mata da cewa ai tuni aka bashi ya cinye.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub