Ƙasar Hausa Sana'a

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sana'o'i a Ƙasar Hausa


Gabatarwa

Sana’a, kalma ce da aka aro ta daga Larabci, kuma take ɗaukar ma’ana ta samar da wani abin amfani ta hanyar hikima a Hausance. Misali, sana’ar ƙira.

A gargajiyance, Bahaushe yana da sana’o’in da yawansu ke da wahalar ƙididdigewa. Daga cikin irin waɗannan sana’o’i akwai manya akwai kuma ƙanana. Sannan kuma masana sun kasa su zuwa kashi uku da suka haɗa da sana’o’in maza, sana’o’in mata da kuma sana’o’in haɗaka ko gamayya.
Sana’o’in maza su ne sana’o’in da maza zalla ne suka fi yin su. Koda an samu mata a ciki to yawansu bai kai a misalta ba. Misali, sana’ar ƙira, fawa, da sauransu.

Sana’o’in mata kuma su ne sana’o’in da mata ne kawai suka keɓanta da yin su. Idan aka ga namiji a ciki irin waɗannan sana'o'i akan kira shi da ɗandaudu. Daga cikin irin waɗannan sana’o’i akwai sana’ar kitso, dafe-dafen abinci, da sauransu.

Sana’o’in gamayya kuma su ne sana’o’in da maza da mata suka yi tarayya a ciki. Daga cikin irin waɗannan sana’o’i akwai kiwo, roƙon baka da sauransu.

Nau'ukan Sana'o'in Ƙasar Hausa

  1. Sana'ar Wanzanci.
  2. Sana'ar Kiwo.
  3. Sana'ar Gini.
  4. Sana'ar Dukanci.
  5. Sana'ar Sussuka.
  6. Sana'ar Fawa.
  7. Sana'ar Noma.
  8. Sana'ar Sassaƙa.
  9. Sana'ar Saƙa.
  10. Sana'ar Kitso.
  11. Sana'ar Ƙira.
  12. Sana'ar Jima.
  13. Sana'ar Rini.
  14. Sana'ar Ginin Tukwane.
  15. Sana'ar Arkomanci.
  16. Sana'ar Farauta.
  17. Sana'ar Su.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub