Sana'ar Ƙira
Gabatarwa
Sana’ar Ƙira tana daga cikin daɗaɗɗun sana’o’in ƙasar Hausa. Maƙera su ke samar da mafiya yawan kayan aikin da sauran masu sana’o’in Hausa ke amfani da su. Gurin da ake yin wannan sana’a shi ake kira maƙera. Haka nan ma mai yin ƙira akan kira shi da maƙeri (mutum ɗaya kena) ko kuma maƙera (jama’u kenan).
Sana’ar Ƙira sana’a ce da ake sarrafa tama da ƙarafa, zinariya ko azurfa, da sauran dangogin ƙarfe a mayar da su abin amfani wanda ka iya zama makami ko ma’aikaci (abin yin sana’a).
Rabe-Raben Ƙira
Sana’ar ƙira ta kasu kashi biyu bisa la’akari da abubuwan da ake ƙerawa. Akwai ƙirar fari, akwai kuma ƙirar baƙi.
Ƙirar Fari
Ƙirar fari ita ce ƙirar kayan alatu (kayan kwalliya na mata kamar ɗan-kunne, sarƙa, da sauransu, da kuma kayan adon ɗaki kamar irinsu kumbo, da kuma kayan adon dawaki, da sauransu) da kuma sauran ƙanan kayan aiki. Maƙeran fari su ke ƙera kayayyaki kamar irin su abin hannu na mata, askar wanzamai, da sauran abubuwan alatu.
Ƙirar Fari
Ƙirar Baƙi
Ita ce gama-garin ƙira. Ta hanyar wannan ƙira ake ƙera kayayyakin amfanin yau-da-kullum kamar irin su fartanya, garma, takobi, da sauransu.
Ƙirar Baƙi
Kayan Aiki
- Maƙera: Ƙarfe ne dunƙulalle, a kanta ake bugun ƙarfen da ake son ƙerawa ya zama wani abu bayan an fito da shi daga wuta.
- Zugazugi: Fatar akuya ce ko tinkiya ake yi mata jima ta musamman sannan a saka mata ƙota da ƙarfe a bakin ƙotar. Da su ake iza wutar ƙira.
- Guduma: Ƙarfe ne ake yi masa ƙota. Da ita ake dukan ƙarfen da ake son ƙerawa bayan an ɗora shi a kan maƙera.
- Masaba: Abin bugun ƙarfe ce da ake yin ta da zallar ƙarfe.
- Awartaki ko Araftaki: Ƙarfe ne ake yin sa dan ɗauko ƙarfe daga wuta.
- Gawayi: Shi ne makamashin wuta.
- Tama: Sinadari ne da ake yin ƙarfe da shi.
- Ƙarfe: Shi ake ƙerawa.
- Kasko: Ana zuba ruwa a ciki da wasu lokutan ake tsoma ƙarfen da ake son rage wa zafi.
- Kurfi: Da shi ake sara ƙarfe.
- Gizago: Ana sassaƙe ƙota da shi idan buƙatar hakan ta taso.
- Matsoni: Da shi ake yin huda (ƙofa) a jikin ƙarfe.
- Madashi: Da shi ake huda ƙota bayan an saka shi a wuta ya yi ja.
Maƙera
Zugazugi
Guduma
Masaba
Awartaki/Araftaki
Kurfi
Gizago
Matsoni
Madashi
Manazarta:
Alhassan A., Musa U.I., da Zarruƙ R.M. (1982). Zaman Hausawa Don Makarantun Gaba da Firmare.
Durumin Iya M.A. (2006). Tasirin Kimiyya da Ƙere-Ƙeren Zamani a kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya. KABS Printing Services (NIG), Durumin Iya, Kano-Nigeria.
Madauci I., Isa Y., da Daura B. (1968) Hausa Custom. Northern Nigerian Publishing Compnay, Zaria-Nigeria.
Yakasai K.I. (Babu shekarar bugu). A San Mutum A Kan Cikinsa (Babu Sunan Maɗaba’a).
Zarruƙ R. M., Kafin Hausa A. A. da Al-Hassan B. S. Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Makarantun Sakandare Littafi na Biyu. University Press, Ibadan.
Tattaunawa da Hussaini Shu’aibu a Ranar 9/11/2016, a Garin Farken Yamma, cikin Ƙaramar Hukumar Minjibir, Jahar Kano a Najeriya.
Hausa
Darrusan HausaSana'o'in Ƙasar Hausa
Sana'o'in Ƙasar Hausa
- Wanzanci.
- Kiwo.
- Gini.
- Dukanci.
- Sussuka.
- Fawa.
- Noma.
- Sassaƙa.
- Saƙa.
- Kitso.
- Ƙira.
- Jima.
- Rini.
- Ginin Tukwane.
- Arkomanci.
- Farauta.
- Su.
Tatsuniyoyi
- Gizo da Noman Gyaɗa
- Gizo da Saniya
- Gizo da Ƙoƙi da Kantu
- Gizo da Ɗanrago...
- Gizo Ɓarawon Gyaɗa
- Gizo da Ɓaure
- Biri da Kura
- Kura da Kare
- Auren Barewa...
- Kuturu, Makaho...
- Alhaji da Hajiya
- Wasu Mutane Huɗu
- Baban Rogaji
- Yarinya da Ƙawayenta
- Mutum da Zabi
- Ƙuda da Kwaɗo
- Ɓarayin Rake
- Maraya
- Ɓarawon Gwal
- Tsiniyama da Lafiyana
- Yusufu da Bala
Bukukuwa
Wasanni
Karin Magana
Wakokin Makaɗa
- Waƙoƙin Makaɗa
- Makaɗan Fada
- Makaɗan Sarauta
- Makaɗan Jama’a
- Makaɗan Maza
- Makaɗan Mata
- Makaɗan Ban-Dariya
- Makaɗan Sana’a
Kayan Kiɗan Hausa
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:
TweetLatsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin