Sarki Musulmi Abubakar Mai Raɓah

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarki Musulmi Abubakar Mai Raɓah


Gabatarwa

Sarkin Musulmi Abubakar II, shi ne Abubakar Mai Raɓah, ɗa ne ga Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo, shi kuma ɗan Shehu Usmanu Mujaddadi. Shi ne sarkin Musulmi na takwas. Mutum ne mai kwarjini gaskiya, adalci, tsoron Allah, sannan kuma tsayayye a cikin harkokin addini.

Abubakar II, ya zamo Sarkin Musulmi bayan rasuwar Sarkin Musulmi Ahmadu Rufa’i. An yi masa mubaya’a a ranar Lahdi 16 ga watan Muharram da Asubahi.

Ya yaƙi garuruwan da suka haɗa da Funtuwa, Madarumfa, da sauran su. Ya rasu ranar Laraba a cikin watan Rabbi’ul Auwal. Ya yi sarauta ta tsawon shekaru biyar da watanni uku. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 68. An yi masa jana’iza bisa sunna sannan kuma aka binne shi Wurno.

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.

Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub