Sarki Musulmi Ahmadu Rufa'i

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarki Musulmi Ahmadu Rufa'i


Gabatarwa

Sarkin Musulmi Ahamadu Rufa’i shi ɗa ne ga Shehu Usmanu Mujaddadi. Mutum ne shi mai karimci, kunya da kuma tausayi ga jama’a da kuma ƙasƙantar da kai da gudun duniya.

Shi ne sarkin Musulmi na bakwai. An yi masa mubaya’a a masallain Wurno, ranar Litinin da Asuba, bayan kwanaki biyar da rasuwar Sarkin Musulmi Aliyu II.

Bayan zamowar sa Sarkin Musulmi, ya dawo da fadar mulkin sa zuwa Sakkwato. Shi ne sarkin da ya fara sabunta ginin masallain Shehu Usmanu Mujaddadi.


Wani sashen Masallaci Shehu Mujaddadi

Ya cika ƙasa da adalci. Iya tsawon mulkinsa sau uku ya taɓa fita wajen Sakkwato. Fitar sa ta farko ita ce zuwa gina Islamiyya; ta biyu kuma zuwa garin Kware dan yaƙar kafirai da suka sauka a garin Kayama; sai kuma ta uku da ya fita zuwa garin Kware, dan yin ta’aziyyar ɗan’uwansa Isa wanda aka fi sani da Autan Shehu ko kuma Isan Kware.

Ya rasu a garin Sakkwato cikin watan Muharram. Ya yi sarauta ta tsawon shekaru biyar da watanni shida. Ya rayu a duniya tsawon shekaru sittin da ɗaya. An binne shi a Hubbaren Shehu da ke Sakkwato a cikin ɗakin da aka binne ‘yar’uwarsa Nana Asma’u.


Ƙofar Shiga Hubbaren Shehu Sakkwato

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.

Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub