Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarki Musulmi Aliyu Ƙarami


Gabatarwa

Sarkin Musulmi Aliyu II, ɗa ne shi ga Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo, shi kuma ɗan Shehu Usmanu Mujaddadi. Shi ne Sarkin Musulmi na shida. Mutum ne shi mai hankali da tsoron Allah.

Ya zamo Sarkin Musulmi bayan an yi masa mubaya’a a masallain Chimmola; bayan kwanaki huɗu da rasuwar Sarkin Musulmi Ahmadu, a cikin watan Jimada Akhir.

Sarkin Musulmi Aliyu II, ya ɗauke fadar mulkinsa daga Chimmola ya koma Wurno. Mulkinsa bai tsawaita ba, duka-duka ya yi sarauta ta tsawon watanni goma sha ɗaya. Ya rasu a garin Wurno a farkon watan Jimada Akhir a ranar Laraba. An yi masa jana’iza bisa sunna aka kuma binne shi a Wurno tare da mahaifinsa da ɗan’uwansa.

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.

Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub