Sarki Musulmi Umaru

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarki Musulmi Umaru ɗan Aliyu


Gabatarwa

Sarkin Musulmi Umar ɗa ne ga Sarkin Musulmi Aliyu, shi kuma ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo, shi kuma ɗan Shehu Mujaddadi. Mutum ne shi mai fasaha da kuma yawan kyauta.

An yi masa mubaya’a ranar Litinin 21 ga watan Zilƙa’ada, a masallain Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo da ke Sakkwato. Shi ne sarkin Musulmi na goma, sannan kuma na farko a cikin jikokin Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo da ma baki ɗayan jikokin ‘ya’yan Shehu Usmanu Mujadaddi. Wato daga kansa salsala ta koma hawa uku kafin Shehu (Umar > Aliyu > Muhammadu Ballo), ko kuma hawa huɗu har Shehu (Umar > Aliyu > Muhammadu Ballo > Shehu).


Masallacin Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo

A iya tsawon mulkinsa ya yi yaƙi da Argungu, da kuma Madarumfa. Haka nan kuma a zamaninsa ne Auzinawa (Azbin) suka yawaita shigowa tare kuma da bayyana al’amuransu, bayan sun kasance suna ɓoye da’awarsu ta sharifanci da suke yi. Sun kasance suna da’awar sharifanta dan su samu damar gudanar da cinikayya a wajen jama’a. Su samu damar shiga lungu-lungu da saƙo-saƙo dan gudanar da kasuwancinsu. Sun samu isa zuwa ga Sarkin Musulmi, suna yi masa hidima a duk shekara idan suka zo.

Ya rasu a garin Ƙauran Namoda a lokacin ganawa da ya saba yi da sarakunan Gabas. Ya rasu a ranar Laraba, 17 ga watan Sha’aban. An kuma yi masa jana’iza aka binne shi a can. Ya yi sarauta ta tsawon shekaru 9 da watanni 10. Ya rayu tsawon shekaru 69 a duniya.

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.

Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub