Azuzuwan Kalmomi
Gabatarwa
A fannin nahawun Hausa, an rarraba dukkanin kalmomin Hausa zuwa aji-aji dan samun sauƙin yin hulɗa da kalmomin. Wannan aji-aji da aka yi musu a wasu lokutan ana kiransa da azuzuwan nahawu.
Dukkan wata kalma Bahaushiya, da ma baƙuwar kalmar da aka Hausantar da ita, an sama mata aji daidai da irin aikin da take yi.
Azuzuwan Kalmomi
Akwai saɓani a tsakanin masana fannin Hausa dangane da suna da kuma karkasa wannan darasi na azuzuwan kalmomi. Wasu daga cikinsu sun kira shi da suna Azuzuwan Kalmomi, wasu kuma suka ce da shi Rukunan Nahawu
Masana kamar irin su, Sani, Muhammad da Rabeh (2000); Yahaya, Zariya, Gusau da ‘Yar’aduwa (1992), sun kira shi da Azuzuwan Kalmomi.
A ta ɗaya ɓangaren kuma akwai Sani (1999), da kuma su Zarruƙ, Kafin Hausa, da Al-Hassan (1987), da suka kira shi da sunan Rukunan Nahawu.
To, kenan azuzuwan kalmomi da kuma rukunan nahawu duka abu guda ne; wato Ɗanjuma ne da Ɗanjummai. Dangane da abin da ya shafi wannan rubutu kuwa, mun kira su da suna Azuzuwan Kalmomi.
Rabe-Raben Azuzuwan Kalmomi
Kamar yadda aka faɗa da farko, masana sun saɓa dangane da adadin azuzuwan kalmomin, saboda haka a wannan rubutun sai zaɓo guda shida da mafiya rinjaye suka yi tarayya wajen zayyano su. Ga su kamar haka:Azuzuwan Kalmomi shi ne rarraba kalmomin Hausa zuwa aji-aji bisa la’akari da irin aikin da kalmar ke yi. Akwai saɓanin masana dangane da baiwa wannan darasi suna. Sani, Muhammad da Rabeh (2000); Yahaya, Zariya, Gusau da ‘Yar’aduwa (1992), sun kira shi da Azuzuwan Kalmomi. Sani (1999); Zarruƙ, Kafin Hausa, da Al-Hassan (1987), su kuma sun kira shi da suna Rukunan Nahawu. Waɗannan mabambantan sunaye kuma da masana suka baiwa wannan darasi ba komai ba ne kamar sunaye Ɗanjuma ne da Ɗanjummai. Dangane da abin da ya shafi wannan rubutu kuma, mun yi amfani da sunan Azuzuwan Kalmomi. A cikin wannan ƙunshi na azuzuwan kalmomi kuma mun samu azuzuwa shida da suka haɗa da suna, wakilin suna, aikatau, bayanau, siffa, da mahaɗi.
Manazarta:
Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo da Koyarwa. Irshad Islamic Publication Cetre LTD. 31, Adelabu Street, Surulere, Lagos-Najeriya.
Jinju M.H. (1981). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company Limited.
Sani M.A.Z. (1999). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.
Sani M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.
Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.
Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.
Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria
Nahawun Hausa
Tatsuniyoyi
- Gizo da Noman Gyaɗa
- Gizo da Saniya
- Gizo da ƙoƙi da Kantu
- Gizo da ɗanrago...
- Gizo ɓarawon Gyaɗa
- Gizo da ɓaure
- Biri da Kura
- Kura da Kare
- Auren Barewa...
- Kuturu, Makaho...
- Alhaji da Hajiya
- Wasu Mutane Huɗu
- Baban Rogaji
- Yarinya da ƙawayenta
- Mutum da Zabi
- Ƙuda da Kwaɗo
- Ƙarayin Rake
- Maraya
- Ɓarawon Gwal
- Tsiniyama da Lafiyana
- Yusufu da Bala
Wasanni
Karin Magana
Wakokin Makaɗa
- Waƙoƙin Makaɗa
- Makaɗan Fada
- Makaɗan Sarauta
- Makaɗan Jama’a
- Makaɗan Maza
- Makaɗan Mata
- Makaɗan Ban-Dariya
- Makaɗan Sana’a
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:
TweetLatsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin