Hakimin Dutse Halilu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Halilu Ɗan Bello 1910 – 1911 (Hakimi)


Gabatarwa

Sarki Halilu Ɗan Bello Bayallige, shi ne Hakimin Dutse na biyu. Naɗinsa ya biyo bayan tsige abokin wasansa (ɗan wa da ɗan ƙani suke; Sarki Suleman 1849 – 1868, wan Sarki Bello 1840 – 1849 ne, dukkansu kuma ‘ya’yan sarki Musa Ahmadu 1819 – 1840 ne) Sarki Haladu Ɗan Suleman.

Abin da ya ci doma, ba zai bar awai ba, guguwar da ta kau da Sarki Haladu, ita ta kawar da Sarki Halilu daga kujerar hakimcin Dutse. Saboda wannan fari da ya gada, maimakon ya ragu, sai abin ma da ya ƙaru, har ta kai ga jama’a suna yin hijira daga yankin na Dutse suna komawa Gaya, Ringim, da kuma Birnin-Kudu dan su ci gaba da rayuwa.

Mr. Bell, wanda shi ne Rasidan na wannan lokaci, ya tsige Sarki Haladu ne daga kan kujerar Hakimci saboda yana ganin cewa ya gajiya wajen tattara kuɗaɗen haraji. Shi a ganinsa, tunda abin ya shafi ɓangaren arewacin masarautar ne, saboda haka bai kamata a ce tattara kuɗaɗen ya taɓarɓare haka ba.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub