Sarkin Dutse Ibrahim II

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ibrahim Ɗan Musa 1894


Gabatarwa

Sarki Ibrahim Ɗan Musa shi ne sarki na talatin da shida a jerin sarakunan Dutse, sannan kuma sarki na takwas a jerin sarakunan Fulani a Dutse. Ana yi masa laƙabi da Maje Fagge. Tun kafin zamowarsa sarki sun saba da shi da Yusufu Galadiman Kano ta dalilin ɗan’uwansa sarkin Dutse Suleman Ɗan Musa (1849 – 1868).

Saboda haka a lokacin da shi Yusuf Galadiman Kano ya fita zuwa Takai shi da jama’arsa, sai shi Ibrahim Ɗan Musa ya bashi dawakai ɗari, da kuma kwari da baka masu tarin yawa a matsayin gudunmawa.

Kasantuwar shi kansa Ibrahim Ɗan Musa da Galadiman Kano Yusufu ciwonsu iri ɗaya ne, sai shi Suleman Ɗan Musa ya ga cewa wannan dama ce a gare shi ta ya haɗa kai da shi Galadiman Kano Yusufu ya samu ƙarin ƙarfin da zai yaƙi sarkin Dutse Salihu Ɗan Ibrahim II Bajallige (1893 – 1894), inda suka haɗu su uku; Suleman ɗan Musa, Galadiman Kano Yusufu, da kuma sarkin Gumel.

Bayan da wannan runduna ta haɗaka ta ci Gaya da yaƙi a watan Agusta 1894, sai Galadiman Kano Yusuf ya yiwa Sarki Ibrahim Ɗan Musa sarautar Dutse, sannan kuma ya aura masa ‘yarsa; wato Sarkin Dutse Ibrahim ya auri ‘yar Galadiman Kano Yusufu.

(Northern Nigerian Publishing Company, 1970), sun ruwaito cewa an kashe sarkin Dutse Ibrahim Ɗan Musa ne a ɗaya daga cikin irin yaƙuwan da suka yi na haɗin guiwa da Galadiman Kano Yusufu, suka ce, “Daga nan sai yaƙe-yaƙe tsakanin Tukur da Yusufu. Tsakanin Fagge da cikin birni kuma ba mai shigowa sai a kashe shi; a rana ɗaya aka kashe Sarkin Dutse Ibrahim da Barden Kano Sulaimanu”.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sarakunan Dutse

Haɓawa

Fulani


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub