Gurmi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gurmi


Gabatarwa

Gurmi, abin kiɗa ne wanda ya ke ɗaya daga cikin kayan isga.

Kayan Haɗin Gurmi

  1. Ƙoƙo ƙarami
  2. Fatar Guza
  3. Almowa: Fatar akuya da dukawa ke gyarawa
  4. Sanda: daga itaciyar kanya ko geza.
  5. Ƙayar aduwa yanzu kuma ƙusa.
  6. Jijiyar dabba yanzu tsirkiya: tsirkiya kuma zare ne na roba da masu kamun kifi ke yin koma da ita.
  7. Jakin gurmi: kara ne na dawa ake yanka shi guntu a ɗora shi a tsakanin tsirkiya da fatar guza bayan an rufata a saman ƙoƙo.


Gurmi


Cikin Gurmi

Yadda Ake Kaɗan Gurmi

Manazarta:


Gusau S.M. (2017). Kayan Kiɗan Hausa. Centuary Research and Publications, Kano – Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.  

Tattaunawa da Umaru a garin Uke ta Jaha Nassarawa ranar Alhamis 14/3/2018. Wanda ya ɗauki kimanin shekaru 20 yana kaɗa gurmi.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub