Shafin Farko

Kwamfuta


Ma’anar kwamfuta

Kwamfuta na’urar laturonik ce wadda ke karɓar bayanai ta sarrafa, ta adana sannan kuma ta bayar da sakamako bisa kulawar softuwayar da aka ɗura mata.

Muhimman Ɓangarorin Kwamfuta

Abin da nake nufi da muhimman ɓangarorin kwamfuta a nan shi ne ɓangarorin da sai an same su ne kwamfuta take iya yin aiki, rashin ɗaya daga cikin su yana haifar da tawaya ga kwamfuta. Baki ɗaya su huɗu ne kamar haka:

  1. Injin Kwamfuta System Unit: Shi ne ɓangaren da ke yin duk aikin da kwamfuta ke yi. Ya ƙunshi ɓangarori mabanbanta sannan kuma kala biyu ne akwai na kwance wanda ake ɗora fuskar a kansa, wato Desktop Model (Hoto na b da ke ƙasa) a Turance da kuma na tsaye wanda ake ajiye shi a gefe ko ƙarƙashin benci, Tower Model (Hoto na a da ke ƙasa) kenan a Turance.
  2. Fuska Monitor: Ita ce ɓangaren kwamfuta da ke nuna maka aikin da kwamfuta ta yi ko take yi. Kala biyu ne: Mai kama da talabijin Cathode Tube (Hoto na a da ke ƙasa) da kuma mai faranti Flat Screen ko LCD (Hoto na b da ke ƙasa).
  3. Kibod Keyboard: Shi ne ɓangaren kwamfuta da ake amfani da shi wajen yin rubutu. Sun kasu kashi uku: PS2 (Hotuna na ƙasa: 1a Kibod 1b kan kibod), USB (Hotuna na ƙasa: 2a Kibod 2b kan kibod) da kuma wireless ko Codeless (Hoto na ƙasa: 3). Dukkansu sun bambanta ne da majona, wato ƙarshen kebir ɗinsa kamar yadda za a gani a hotunan da ke ƙasa:
  4. Mawus Mouse: Shi ne ɓangaren da ake amfani da shi wajen zaɓi da bai wa kwamfuta umarni. Yana da bambanci ta fuskacin majona wanda ciki akwai PS2 (Hoto na ƙasa: 1), USB (Hoto na ƙasa: 2) da kuma Wireless (Hoto na ƙasa: 3) kamar kibod. Duba hotuna na ƙasa:

Waɗannan ɓangarori da aka zayyana a sama guda huɗu su ne ainihin tushen kwamfuta waɗanda idan basu haɗu ba to kwamfuta bata cika ba. Amma dukkan sauran sukan zo ne bisa buƙata.

Manazarta:


Tsangarwa A.M. (2010). Kwamfuta a Sauƙaƙe, Sabon Bugu. Tsangarwa ICT Limited, Kano-Nigeria.