Bitar Ma’anar Kalmar ‘Hausa’

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Bitar Ma'anar Kalmar 'Hausa' A Ƙarni Na 21...


Yusuf Nuhu Inuwa
School of Languages, College of Arts, Science and Remedial Studies, Kano
+2348060444074/yusufnuhu84@gmail.com


Tsakure

Masana sun yi ta yunƙuri a baya wajen rawaito asalin kalmar Hausa amma har yanzu ba a cimma wata ƙwaƙƙwarar matsaya game da inda tushen kalmar ya tusgo ba. Domin tarihin Hausawa da na samuwar kalmar ta Hausa al'amari ne da zai yi wuya a iya haɗuwa bisa matsaya ɗaya sakamakon rashin tabbataccen rubutun da za a iya dogara da shi wajen sanin haƙiƙanin yadda ƙasar Hausa ta kafu da bayanin mazauna cikinta na farko da yadda al'amura suka cigaba da wakana daga zamani zuwa zamani; illa iyaka a cigaba da kintatowa har zuwa sa'ar da bincike zai tabbatar da gaskiyar yadda al'amarin yake. Amma idan aka jingine batun asalin kalmar to za a iya kallon ma'anar Hausa ta mabambantan fuskoki kamar yadda Ibrahim (1978) da Ɓaɓura (2008) suka kalle ta a matsayin kalma mai iya ɗaukar ma'anar harshe da mutanen da suke magana da harshen da kuma ƙasar da ake amfani da harshen. Bisa irin waɗannan bayanai ne aka ƙara da cewa: Hausa kalma ce mai faffaɗar ma'ana da take wakiltar Hausawa da harshensu da azancinsu da ƙasarsu da kuma nazarin al'amuransu. Wato kalma ce da ta ƙunshi mabambantan ma'anoni a ƙalla guda biyar masu alaƙa ta ƙut da ƙut da junansu, musamman ta fuskar jama'a da yaren da suke magana da shi a matsayin harshensu da dabarun sarrafa tunani cikin harshen nasu da ƙasar da suke tutiya da ita a matsayin mazauninsu na dindindin da harkar nazari a fagen ilimin harshe da adabi da al'adu na Hausawan a makarantu da kwalejoji da jami'o'i a faɗin duniya.
Mahimman Kalmomi: Bita; Hausa; al'umma; harshe; azanci; ƙasa; nazari; ƙarni na 21.

Latsa nan ka Juyi Takarda


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub