Jiya da Yau, a Duniyar Makaɗan Fada

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Jiya da Yau, a Duniyar Makaɗan Fada


Ibrahim Muhammad
birninbagaji4040@gmail.com
+2348091503592, +2347088700562


Tsakure

Aduk lokacin da ake son ganin tarihin wata al’umma, ci-gabanta da matsalolinta ana komawa ne kai tsaye ne kan adabinta, ta nan ne ake fahimtar al-adunta da dabi’unta. Makadan fada sun zama wani kundi na adana tarihin Masarauta da Sarautun kasar Hausa da Zamantakewa da fadi-ta shi da gwagwarmayar da ake yi a fada. Makadan fada suna shiga irin ta Sarakai haka abin kidansu sun kevanta ne da wakokin fada. Yau da gobe bata bar kome ba. Kwanci tashi sauyi ya zo a duniyar mawakan fada aka bar jiya aka wayi gari a yau da muke saboda yanayin da zamani ya zo da shi ta sanadiyyar cudanyar da al’ummar kasar Hausa ta yi da baki. Wannan ta sa aka sami karin Turakan wa kar fada bayan Turakun farko. Sannan an sami kari kan muhallan da ake rera wakar gargajiya a yau.

Latsa nan ka Juyi Takarda


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub