Ƙa'idojin Rubutu
Gabatarwa
Ƙa’ida, ita ce doka, wacce duk wanda ya saɓa, to ya kauce hanya. Hausa, a matsayinta na babban Harshe daga cikin manyan harsuna a duniya, ta kasu zuwa Hausar Baka da kuma Hausar Rubutu.
Hausar baka, ita ce wacce ake magana da ita, wacce kuma take da kare-kare masu yawa. Jigajigan cikin kare-karen su ne waɗanda ake amfani da su a manya kuma daɗaɗɗun masarautun Hausa da suka haɗa da Kano, Gobir, Daura, Zazzau, Katsina sannan kuma daga baya Sakkwato da sauransu.
Ita kuwa rubutacciyar Hausa, ita ce Hausar da ake rubuta dukkan wani rubutaccen abu a cikin Harshen Hausa. Ita ce Hausar da take da ƙa’idojin rubutun Hausa. Samuwar wannan ƙa’idoji na rubuta Hausa a bokonce, shi ne ya samar da Daidaitacciyar Hausa. Waɗannan ƙa’idoji da ake kiyayewa su ke mayar da rubutu ya zama ya isar da cikakken saƙon da ake son ya isar. Shi ke saka rubutu ya zamo mai daɗin kallo da kuma karantawa da sauransu. A wannan rubutun da mai karatu yake karanta za mu duba waɗannan ƙa’idojin:
Manazarta:
Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa (Yadda Yake Da Yadda Ake Yinsa) Don Masu
Koyo da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adelabu Street, Surulere, Lagos-Nigeria.
Jinju M.H. (2007). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing
Company L.T.D., Gaskiya Building, Zaria, Kaduna-Nigeria.
Sani M.A.Z, Muhammad A. da Rabeh B. (2000). Exams Focus Hausa Language
Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC,
Ibadan – Nigeria.
Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M. (2007). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.
Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Uku.
University Press PLC, Ibadan-Nigeria.
Ƙa'idojin Rubutu
Tatsuniyoyi
- Gizo da Noman Gyaɗa
- Gizo da Saniya
- Gizo da Ƙoƙi da Kantu
- Gizo da Ɗanrago...
- Gizo Ɓarawon Gyaɗa
- Gizo da Ɓaure
- Biri da Kura
- Kura da Kare
- Auren Barewa...
- Kuturu, Makaho...
- Alhaji da Hajiya
- Wasu Mutane Huɗu
- Baban Rogaji
- Yarinya da Ƙawayenta
- Mutum da Zabi
- Ƙuda da Kwaɗo
- Ɓarayin Rake
- Maraya
- Ɓarawon Gwal
- Tsiniyama da Lafiyana
- Yusufu da Bala
Wasanni
Karin Magana
Wakokin Makaɗa
- Waƙoƙin Makaɗa
- Makaɗan Fada
- Makaɗan Sarauta
- Makaɗan Jama’a
- Makaɗan Maza
- Makaɗan Mata
- Makaɗan Ban-Dariya
- Makaɗan Sana’a
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:
TweetLatsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin