Bafilatani Ya Sha Madara

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Muƙyaƙyata: Bafilatani Ya Sha Madara


A wani gari, akwai wani Bafulatani da yake zuwa sayayya wani kanti. Wata rana sai ya je ya sayi madara domin ya sha shayi. Da ya je gida ya zazzage madarar nan a cikin shayi sai ya raina yawan madarar saboda ganin girman mazubin madarar da ya yi kafin ya saya.  Saboda haka sai ya raina yawan madarar.

Da ya sake komawa wannan kantin wata rana domin ya sake sayen madarar nan, sai ya tsinkayi abun wanki; wato omo mai suna Bimbo Fresh wanda launin garinsa fari ne fat, kamar madara. Sai Bafulatanin nan ya nuna omon nan ya ce shi za a bashi. Mai kanti kuma ya ɗauki omo ya bai wa Bafulatani, shi kuma ya karɓa ya koma gefe.

Da aka zuba wa Bafulatanin nan shayi, sai ya juya baya ya buɗe wannan omo ya zazzage a cikin ruwan shayi. Yana shan shayi, yana jin zafi a cikinsa da ƙirjinsa. Can da zafi ya yi yawa sai Bafulatanin nan ya magantu, ya kuma nemi sanar da halin da yake ciki. Sai ya ce da mai kanti: “Wannan wasshe irin madara ki ka bani mai ƙarfi haka?” Sai mai kanti ya amsa masa da cewa ai ba madara bace omo ne. Da Bafilatani ya ji an ce abin da ya sha ba madara ba ce omo ne, sai ya ce: “Wayyo na mutu” ak ce da shi me ya faru? Sai ya ce: “Wannan omon ci na zuba a cayin nan na ca, ji nake madara she. Do Allah ku yi min rai ku kai ni gurin can magani”. Daga nan sai ya dafe cikinsa yana ta sowa.


Labari Daga:
Sunusi Abdullahi, wanda aka fi sani da Kwamanda, Rimin Kebe, Kano. 09027362322


Ana iya turo labari domin a wallafawa ta:
Was-af: 0803 964 8244 (+234803 964 8244)
Imel: rumbunilimi@gmail.com


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub