Rumbun Ilimi - Rubutun Zube

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Rubutun Zube


Gabatarwa

Rubutun zube, ɗaya ne daga cikin muhimman na’ukan adabin zamani. Shi ne ma kusan rubutun da aka fi yi, abu ne da ya haɗiye abubuwan da suka haɗa da rubututaccen labari, tatsuniya, karin magana da sauran makamantansu kamar yadda za a gani a wannan rubutu.

Ma’anar Rubutun Zube

Masana fannin Hausa, sun baiwa rubutun zube ma’anoni mabambanta gwargwadon fahimtarsu. Daga ciki akwai Farfesa Ɗangambo (1984), da ya kalle shi a matsayin “duk wani rubutu ko wata wallafa da ba waƙa ba kuma ba wasan kwaikwayo ba”.

Rassan Rubutun Zube

 1. Rubutaccen Labari.
 2. Tarihi.
 3. Ƙagaggen labari, a cikinsa ake samun tatsuniya, hikaya, da almara.
 4. Karin magana.
 5. Sauran rubututtuka da ake yi game da abubuwan da suka shafi rayuwar Bahaushe matuƙar dai ba waƙa ce ko wasan kwaikwayo ba, to ana iya kiransa rubutun zube, bisa dogaro da waccar ma’ana ta Farfesa Ɗangambo (1984).

Misali:
Wata rana, Ado ya shiga kasuwar Sabon Gari da ke Kano a Nijeriya domin ya sayi zogale da ƙarago/ƙuli-ƙuli domin a yi masa kwaɗo. Ya yi ta gararamba a kasuwar nan har sai da ya gaji.

Can da ya ga uwar bari, sai ya tambayi wani mai shago a kasuwar ya ce da shi, “malam barka da kasuwa, dan Allah malam ina zan samu zogale a wannan kasuwar?” Sai mai shagon ya ce da shi, “gaskiyar lamari samun zogale a wannan kasuwar da kamar wuya, gurguwa da auren nesa. Amma ka tafi Kasuwar Rimi ko Kasuwar ‘Yankaba, can kam na san za ka samu”. Da Ado ya ji haka sai ya ce, “Kash! Rashin sani ya fi dare duhu, ka ga kuwa yanzu daga Gunduwawa na fito, ai da na san haka da na fara sauka a Kasuwar ‘Yankaba, amma na gode, bari na yi azama na tafi Kasuwar Rimi”.

Daga nan sai Ado ya fice ya tafi Kasuwar Rimi domin sayen zogale da ƙuli-ƙuli. Yana zuwa kuwa, abin da zai fara gani da farko ita ce wata gyatuma ɗauke da ƙwaryar zogale a kanta za ta masaya. Da ganinta sai ya ce da gyatumar nan ta kawo ya rage mata kaya, ta kuwa bashi ya ɗauka mata, ta wuce gaba yana biye da ita har suka kai masaya.

Da isarsu masaya, bayan ta buɗe hajarta, sai Ado ya ce, yana son zogale na naira ishirin, gyatuma ta ɗaura masa zogale kusan na naira ishirin da biyar saboda jin daɗin taimaka mata da ya yi. Bayan kuma ya sayi zogale ya tsallaka ɗaya ɓarin ya sayi ƙarago/ƙuli-ƙuli na naira biyar ya tafi abinsa.

Da isowar Ado gida sai ya yi sallama, yara suna jin sallamarsa suka amsa masa sannan suka ruga, suka tarbe shi suna cewa, sannu da zuwa baba, suka karɓi kayan da ke hannunsa sai gurin uwarsu. Uwargida ta karɓi kaya ta kuma yi wa mai gida sannu da zuwa, sannan ta tashi, ta saka yara a gaba suka zuge zogale, ta dafa zogale, sannan ta kawo ƙarago/ƙuli-ƙuli, barkono, da daddawa ta daka su a turmi, sannan ta zuba garin a ƙoƙo, ta dama da ruwa, ta kawo zogalen nan ta zuba, ta yi musu kwaɗo mai daɗi.

Bayan da ta gama, sai ta zuba wa mai gida nasa, sannan sauran yara ma ta zuba musu nasu; mata a mazubi guda haka nan ma maza nasu mazubin dabam. Kowa ya ci wannan zogale ya yi hani’an.

Tarihin Rubutun Zube

Rubutun zube ba daɗaɗɗen fannin adabi ba ne (Junaidu da ‘Yar’aduwa, 2002), idan ma abin a fara ɗauko tarihin rubutun zube ne daga lokacin da Hausawa suka fara rubuta shi da kansu, to ana iya cewa rubutun waƙoƙi ya grime shi (Ɗangambo, 1984).  Muna iya ƙarfafar wannan huja ta Farfesa Ɗangambo (1984), da rubutun Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992), da suka ce asalin rubutun littattafan labaru na Hausa yana farawa ne daga shekarar 1930, lokacin da Gwamnatin Jahar Arewa ta kafa hukumar fassara mai suna Translation Bureau bayan yawaitar makarantun boko a yankin arewa. Suka ci gaba da bayyana cewa a ƙarƙashin wannan hukuma aka wallafa littattafai guda biyu:
 1. Dare dubu da ɗaya.
 2. Labarun Hausawa da Maƙwabtansu.

Haka nan kuma bayan shekara uku aka canjawa hukumar suna ta koma Literature Bureau inda ta samar da littattafan da suka haɗa da:

 1. Ruwan Bagaja, na Alh. Abubakar Imam.
 2. Ganɗoki, na malam Bello Kagara.
 3. Shehu Umar, na Alh. Abubakar Tafawa Ɓalewa.
 4. Idon Matambayi, na malam Muhammadu Gwarzo.
 5. Jiki Magayi, na malam Tafida da R.M. East.

Sannan kuma daga baya wasu zaƙaƙuran masana kuma Hausawa suka duƙufa wajen rubuta waɗannan littattafan:

 1. Nagari na Kowa, na Alh. Abubakar Imam.
 2. Iliya Ɗan Maiƙarfi, na Ahmadu Ingawa.
 3. Da’u Fataken Dare, na Tanko Zango.
 4. Bayan Wuya Sai Daɗi, na Abdulmalik Mani.
 5. Tauraruwa Mai Wutsiya, na Umaru Dembo.
 6. Tauraruwar Hamada, na Sa’idu A. Daura.
 7. Gari ya Waye, na Muhammadu Balarabe Umar.

Kenan, a taƙaice daga shekarar 1930 da waɗannan rukunin masana suke ganin Bahaushe ya fara rubuta labari da kansa, zuwa yau 2016, rubutun zube shekarunsa 86 da haihuwa.

Nazarin Rubutun Zube

Masu nazari na bayar da himma wajen zurfafa tunani domin fitar da wasu fa’idoji game da wani rubutu da aka samar. To wai tayaya suke yin wannan aiki ne? Ka ga, idan kana son nazartar rubutun zube, sai ka fara la’akari da waɗannan abubuwan:
 1. Jigo: Jigo shi ne asalin darasin da aka gina labarin a kansa; wato saƙon da ake son isarwa a cikin labarin. Akan gina ƙagaggun labarai akan abubuwan da suka shafi jarumtaka, soyayya, haƙuri, kyautatawa, nishaɗi, da sauransu. Misali, idan muka ɗauki littafin Iliya Ɗan Maiƙarfi na Ahmadu Ingawa, za mu ga cewa jigonsa shi ne jarumtaka. Wato a kan jarumtaka aka rubuta littafin. Sannan kuma idan muka lura da ɗan gajeren labarin da aka kawo a sama, za mu ga cewa jigonsa shi ne kyautatawa.
 2. Zubi da Tsari/Salo: Zubi da tsarin labari a nan yana nufin yadda shi marubucin ya shimfiɗa labarinsa tun daga farko harzuwa ƙarshe. Abubuwan da ake dubawa a nan su ne yanayin yadda aka jejjera gaɓoɓin labarin, shin akwai yarjejeniya a tsakaninsu ko akwai bauɗiya. Abin nufi shi ne cewa gaɓar farko ta labarin tana ƙarfafar gaɓa ta biyu ne har zuwa ƙarshen labarin kokuwa akasin haka ne. Misali, idan aka lura da misalin da ya zo a sama, Neman zogale ne ya kai Ado Kasuwar Sabon Garin Kano a Najeriya, kuma da bai samu ba dukkan sauran gaɓoɓin da suka zo sun ɗoru ne a kan neman zogalen har sai da aka kai gaɓar da aka dafa shi aka ci sannan labarin ya ƙare.
 3. Salon Sarrafa Harshe: Abin da ake nufi da salon sarrafa harshe shi ne irin yadda marubucin ya isar da labarin, akwai kwan-gaba-kwan-baya cikin labarin? Ko kuwa ma labarin yana tsittsinkewa daga nan ya fita ya koma can? Da sauransu. Sai kuma amfani da Harshen Hausa wajen rubuta labarin nasa, shin ya yi amfani da sassauƙar Hausa mai sauƙin fahimta ko kuwa a’a? Sannan ya yi amfani da gwanintar harshe kamar irin su karin magana, habaici, gatse da sauransu waɗanda ke ƙarawa rubutun daɗin karantawa ko kuwa? Misali, da aka ce da Ado zai iya samun zogale a Kasuwar ‘Yankaba ko Kasuwar Rimi sai ya ce, “Rashin sanin ya fi dare duhu” wannan karin magana ce kuma idan aka lura za a ga ta ƙarawa rubutun kyau da daɗin karantawa. Shigo da waɗannan cikin rubutu su ake nufi da sarrafa harshe.
 4. Halayyar Jama’ar Cikin Labarin: A nan ana nufin waɗanne irin halaye jama’ar da aka saka a cikin labarin suke da ita? Shin ta yi daidai da Jigon Labarin kokuwa ta fanɗare. Misali, tunda jigon Labarin Ado shi ne kyautatawa, to idan aka lura za a ga cewa, shi ya fara kyautata hali ta hanyar tambaya, sannan mai rumfa ya kyautata masa ta hanyar ɗora shi a turbar da ta dace. Haka nan da ya je kasuwa ta biyu, ya kyautatawa gyatuma ita ma kuma ta kyautata masa. Sannan da ya koma gida ya kyautata musu ta hanyar fara yi musu sallama sannan suma suka kyautata masa da tarba.
 5. Tauraro: Shi ne mutumin da gundarin saƙon labarin ya bayyana daga gare shi. A labari na sama Ado ne tauraron labarin. A kan samu wani mutum ya yawaita fitowa a labari amma kuma ba shi ne tauraro ba. Sannan kuma a mafiya yawancin lokuta, tauraro kan bayyana tun daga farkon labari har zuwa ƙarshe.

Ta bin waɗannan hanyoyi ne mai nazarin rubutun zube zai iya fahimtar inda akalar rubutun ta saka gaba, ya gane a kan wane jigo aka ɗora wannan labarin? Wanne darasi ko darrusa ake son koya daga ciki? Da sauransu.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zungur A. M. S. (1968). Waƙoƙin Sa’adu Zungur. The Northen Nigerian Publishing Company Ltd, Zariya – Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub