Rumbun Ilimi -Adabin Zamani

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Adabin Zamani


Gabatarwa

Bayan zuwan Fulani ƙasar Hausa, sai aka fara samun canji dangane da yadda Hausawa suke gudanar da rayuwarsu, kama-kama har shigowar Larabawa da kuma Turawa. Daga cikin irin waɗannan canje-canje da aka samu, sai ya zama akwai karatu da rubutu, saboda haka sai salo da sigar Adabin Bahaushe ya canja, ya zama ana rubuta wasu abubuwan. Waɗannan abubuwa da ake rubutawa su suka samar da wannan Adabi da aka kira da Adabin Zamani. Kusan shi wannan adabi ya ƙunshi abubuwa ne kamar irin su rubutattun waƙoƙi, rubutun zube, da kuma rubutaccen wasan kwaikwayo.

Ma’anar Adabin Zamani

Farfesa Ɗangambo (1984) ya ce, “Adabin zamani adabi ne wanda zamani ya kawo; wato da can kafin Zuwan Musulunci da zuwan Turawa babu shi”.

Dangane da samuwarsa kuwa, Junaidu da ‘Yar’aduwa (2002), sun bayyana cewa adabin zamani ko rubutaccen adabi ya samu ne bayan zuwan addinin Musulunci da kuma lokacin zuwan Turawa ƙasar Hausa. 

Rabe-raben Adabin Zamani

Ɗangambo (1984), Zarruƙ, Kafin Hausa, da Al-Hassan (1987), Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992), da kuma Junaidu, da ‘Yar’aduwa (2002), duk sun haɗu a kan cewa adabin zamani ko rubutaccen adabi ya kasu zuwa gida uku kamar haka:

  1. Rubutattun Waƙoƙi.
  2. Rubutun Zube.
  3. Rubutattun Wasannin Kwaikwayo.

Amfanin Adabin Zamani

Gudunmawa da adabin zamani ko rubutaccen adabi ya bayar game da rayuwar Hausawa yana da yawa sosai. Kaɗan daga ciki akwai:

  1. Nishaɗi: Akan samu nishaɗi ta hanyar karanta rubutattun labarai, waƙoƙi da sauransu.
  2. Adana tarihi, al’adu, da sauransu: Adabin zamani shi ne nagartacciyar hanyar taskace al’adu da sauran abubuwan da suka shafi rayuwa. Misali, idan aka rubuta labari ko tarihin wani abu da ya shafi Bahaushe, yiwuwar jirkicewarsa bai kai na hanyar isar da saƙon kunne ya girmi kaka ba. Da zarar an samu isuwa ga rubutun farko na asali za a gane cewa an cire ko an ƙara.
  3. Ilimantarwa: Bayyanannen abu ne cewa rubutaccen adabi hanyar ilimantarwa ce. Ko ba komai, shi kansa rubutun wani ɓangare ne na ilimi, saboda haka kenan karanta rubutaccen adabin ma shi kaɗai ilimi ne, bayan kuma ɗimbin hikimomin da za a iya samu a ciki.
  4. Gargaɗi: Adabin zamani hanya ce ta gargarɗi da kuma jan kunne. Akan isar da wannan saƙo na gargaɗi ta hanyar wasan kwaikwayo da sauransu.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub