Rumbun Ilimi - Waƙar Mumafunci

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Waƙar Mumafunci Malam Salihu Kwantagora


Ya Rabbana, Jalla mai ƙudura da adalci,
              Kai ne ka yo ɗaukaka, ka halicci ƙanƙanci.

Ka tsare mu sharrin ɓatattu, masu sa fitina,
              A gari, a kan aikin da su kai, munafunci.

Lalle abin ga da ban tsoro da mamaki,
              Duk galibinmu mutanen yanzu mun ɓaci.

Ka ga saurayi majiyin ƙarfi yana yawo,
              Ya kasa samun sana’a ban da shashanci.

Sai bin gari da rawan ƙwambe abin kunya,
              To, me ka je yi a ofis, ce munafunci.

Im banda ka je munafunci, da kinibibi,
              Zauna gidanka ka zam yaƙi da lalaci.

Zauna ka nemi sana’a wadda za ka riƙa,
              Ka bar yawan tsegumi, da yawan munafunci.

Ka ga maigida da iyali gas hi ba aiki,
              Sai bin gidajen mutane don munafunci.

Ka je ga alƙali, ka ji duk asirinsa,
              Ka kai ga Sarkin gari, don annamimanci.

In an gane ka a ce, “Ku tsaya tukun ya wuce”,
              Kwaɗayin kwabonka shi jawo ma wulaƙanci.

Shi annamimi, abin a guje shi ne da gudu,
              Cutarsu ɗai da maciji, babu bambanci.

Gaba ta tashi tsakanin masu soyayya,
              Duk babu mai yinsa sai sarkin munafunci.

Tafi ofishin “Gaskiya” ka ga kyan zama, malam,
              Don babu ƙwanji, da jin zafi, da makirci.

Mataimakan Edita, kai har da shi Edita,
              Sun kyauta halin zamansu da ba munafunci.

Babba da yaro abin su zamansu zak kyawo,
              Duk wanda kag ganshi can ya yaƙi jahilci.

Kai, annamimun mutum kam bai ji daɗi ba,
              Allah wadan wanda yattsare yin munafunci.

Cutarsa ta fi gaban a ƙididdige ta duka,
              Ɓarnar wuta ma tana bayan munafunci.

Babban abin tsoro ɗaya wanda za ni faɗi,
              Ka ga malamai masana su tsaya munafunci.

Kuma malami ya ƙi yin aikinsa malanta,
              Ya kutsa kansa ga son mulki da zalunci.

Allah ka sa mu fi ƙarfin zuciyoyinmu,
              Ka sa mu wanye cikin sutura, cikin ‘yanci.

Allah Ta’ala da iko nai da Girmansa,
              Yaɓ ɓaci jimlar waɗanda ka yin munafunci.

Manazarta:


NNPC (1981). Waƙoƙin Hausa. Northern Nigerian Publishing Company Ltd, Zaria, Kaduna - Najeriya.

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub