Rumbun Ilimi - Waƙar Yabon Ubangiji

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Waƙar Yabon Ubangiji: Mu'azu Haɗejia


Na fara talifi da sunan Ubangiji,
              Subhanahu Mannanu babu kamar Shi.

Komi ka gan shi a duniya farko garai,
              Ko ka gaya mini Rabbu waffare Shi?

Duk wanda yai farko akwai ƙarshe garai,
              Sai rai guda ne babu mai kaushe Shi.

Balle shi kwanta har a je dubo Shi,
              Rayin da baya fargabar tsoron wani.

Balla a ce wani za shi je shi buge Shi,
              Rayin da bai nuna shina gurbi kaza

Kuma ba muhalli inda za ka biɗe Sh,
              Ba za ka ce ya sauka yau a jiha kaza

Kuma gobe za Shi Shi sauka can al’arshi,
              Shi Rabbu rayi ne guda ɗaya Wahidun.

Duka inda ka neme shi ka same Shi,
              Rayin da bai gajiya bare shi yi gyangyaɗi.

Hali na gajiyawa yana ga wanin Shi,
              Rayin da ba Ya cin abinci bare Ya sha.

Balle Shi je ta kwaɗayi wurin mai ba Shi,
              Rayin da babu uwa gare Shi bare uba.

Shi ba Shi ɗa balle a san jikanShi,
              Shi ba a cewa wance ce mata tasa.

Balle ta je ta yi kwalkwasa a gaban Shi,
              Ba Ya buƙatar ƙwarƙwara da makulliya.

Balle a sami jakadiya a gidanShi,
              Ba wanda zai ce ga gidanShi a gu kaza.

Balle ka je ka a ce da kai ya tashi,
              Albaulu, gayiɗu ko jima’i ba Shi yi.

Shi hadisi ne ajizi ne mai yin shi,
              Da zai yi wannan, ka sani kai baka yi.

Da ka ke ko, ka san ba buƙata gare Shi,
              Ba Ya saye, ba Ya sayarwa Rabbana.

Balle a ce wani na biyatai bashi,
              Mun san Shi sosai inda siffofi Nasa.

Ƙwayar idanu ta gaza ta gane Shi,
              Sarkin da ba Shi waziri ba Shi da hakimi.

Shi bashi alƙali balle muhutinShi,
              Ba Ya buƙatar kwanciya kan shimfiɗa'

Balle a san wani wanda zai tashe Shi,
              Ba za a ce maka bai fito ba ka dakata.

Duka lokaci kowa shina nan gunShi,
              IkonSa ne a’ala a kan iko duka.

Ba mai hukunci wanda za shi kira Shi,
              Shi ba a kai mai tsegumin laifin wani.

Da gani da ji aikinSa ne ba fashi,
              Ba Ya ganin ƙyashin abin da ka mallaka.

Kome ka samu shi Ya ba ka da sonShi,
              Mai ba ka duk bai ba ka im bai ba ka ba.

KyautarSa in Ya ba ka ba ta tashi,
              Kyauta gare Shi dare da rana da safiya.

Shi ba Shi ƙosawa da mai roƙon Shi,
              Kuma cinka, shanka, tufarka Shi zai ba ka su.

Ɗebe zaton wani za shi ba ka kamar Shi,
              Wasu Ya gama musu tasu kyauta duniya.

Can lahira ba sa biɗa a gare Shi,
              Wasu Ya hana su a duniya ba su damu ba.

Can lahira zai ba su tasu da dushi,
              Wasu ko ya ba su a duniya har lahira.

Da ma Shi samu cikin su don al’arshi,
              Wasu Ya hana su rabo na ɗakin duniya.

Kuma lahiram ma ya hana su abin Shi,
              Shi ne ka aikata yadda Ya so Wahidun.

Don babu mahalukin da za shi kwaɓe Shi,
              Ni’imarSa ta gajiyar da duk mai lasafi.

Haka nan azabobinSa mai al’arshi,
              Kowa ya ce zai ba ka ba shi da hamzari.

Kome ya danƙa ma sila aka ba shi,
              Kyautar da ya yi a duniya har lahira.

Ba ta ragin kome cikin taskarShi,
              Fitila guda da za a kunna guda dubu.

A jikinta hasken bai rago a gare Shi,
              Rana guda ɗaya ce, wata ɗaya ne ku san.

Kowa gidanai za a san haskenshi,
              AyarSa ce wannan ga duk mai hankali.

AikinSa ya gajiyad da mai koyin Shi,
              Shi ne Saburu, Ubangiji haƙuri garai.

Kome mutum shi ka aikata Ya san shi,
              Hairan da sharran wanda duk aka aikata.

Da mala’iku da suke rubutu don Shi,
              Dukkan abin da ka aikata su sun gani.

Kuma sun rubuta sai a ranar tashi,
              Ba sa kawar da ganinsu ko ji da’iman.

Ba ƙayyadewar lokacinsu na tashi,
              Baka san su ba, ba sa biɗar sabo da kai.

Su ba su karɓar toshiya ko dashi,
              In kai kana barci ka san su basu yi.

A gabansu zaka yi har ta kai ka ka tashi,
              Kowa abin da ya aikata ran lahira.

Ran nan ake jimla a ba shi abinshi,
              Wani za a ba shi kitabihi biyaminihi.

Wannan rabon Aljanna ne a gare shi,
              Allah ka ƙaddara namu ma biyaminina.

Wa bi hurumatit Tijjani don kakanshi,
              Wani ko ta ƙirji za a hudo zaharihi.

Hannun hagun san nan a bashi abinshi,
              Allahu ahfizna bi jahil Musɗafa.

Wa bi jahi Annabi Musa don sandarshi,
              La haira illa hairuhu Rabbul wara.

Subhana tsarki ya tsaya a gare Shi,
              Sarkin da ba shi fushi balle shi yi ɓaɓɓaki.

Haƙuri gare Shi Ubangijin Al’arshi,
              Mai bai wa kowa, ba a cewa ya hana.

Kowa ya ce bai ba shi ya saɓe Shi,
              Wuta da Aljanna da cuta da lafiya.

Ko ka gaya mini wanda ya yi su ban da Shi?
              Faƙrun da rizƙun duk tafarkin Jalla ne.

Mutuwa da rayawa ina wani ban da Shi?
              Haka nan ƙishi, yunwa, da shayarwa da ci.

Wa za shi haddasa duk waɗannan ban da Shi?
              Ubangijinka idan ya sa maka arziƙi.

Kome baƙin ran ‘yan’adam sa baka shi,
              Duka duniya in sunka so ka da arziƙi.

Idan Ya sa ma faƙru ba mai baka shi,
              Haulun da ƙuwwa duk garai suka tattare.

Subhanahu Mannanu babu awa Shi,
              Halwun da murrun duk gare Shi suke fita.

Sarkin da ba wani wanda zai Masa kishi,
              Can suratul ihilasi ga ayarSa nan.

Shi Wahidul-Ƙahharu ba na biyun Shi,
              Sarkin da ba Shi wakili ba shi muƙaddashi.

Ba Ya biɗar wani taimako a gare shi,
              Ba Ya tuwo balle Ya nemi na cefane.

Shi ba Shi tarawa saboda zuwa gaba,
              Domin idan ya tsufa sa tonye Shi.

Kuma ba Ya tara wa shari’ar zamani,
              Domin Ya ɗau lauya shi ka da wanin Shi.

Ba Ya biɗar lada da neman tallafi,
              Kowa ya aikata aikatau don kanshi.

Ƙarshen ‘Izazul’ in ka duba ka gani,
              AyarSa ce ƙaulinSa ba ya tashi.

Sarkin da ba wani wanda zai masa bincike,
              Mai bincike ma Rabbu shi ya yi shi.

Babban Gwani mulkinSa ba ƙarami ba ne,
              Mulkin hawa mulkin da babu kamar shi.

Huwa Haliƙud dayyanu laisa kamislihi,
              Gausun Giyasun Ubangijin Al’arshi.

Shi ke da iko babu mai iko da Shi,
              Shi ke da girma babu wanda ya kai Shi.

Dukkan mutum mutakabbiri ƙarya shi ke,
              Ya san da wanda ya fi shi, wanda ya yi shi.

Alkibriya’u li Rabbana sifatun bihi’
              Duba cikin Ta’alimu a same shi.

Kowa ya ce zai taƙama ba tasa ba,
              Shi ya ɓace kuma babu mai nemo Shi.

Kaitonka wawa mai gada da gadar wani,
              Ka mance wanda ya yi ka shi yay yi shi.

Allahu kai tsira ga Ahmadu Musɗafa,
              Wa li alihi wa sahabihi domin shi.

Shi ne Muhammadu wanda anka yi duniya,
              Ya zuwa makoma lahira domin shi.

Haka nan azaba an yi don maƙiyan shi ne,
              Aljanna domin wanda ke ƙaunar shi.

Ni ne Mu’azu Haɗeja ni na yi wallafar,
              Haza a ƙallu minal ƙalili yabon Shi.

Baiti tamanin ne a nan muka dakata,
              Ƙirga su sosai don ka san jimlar shi.

Manazarta:


Haɗejia M. (1982). Waƙoƙin Mu’azu Haɗejia. Northern Nigerian Publishing Company Ltd, Zaria, Kaduna - Najeriya.

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub