Rumbun Ilimi - Waƙar Hawainiya

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Waƙar Hawainiya: Tijjani Tukur Yola


Idan ban da ƙarya rashin kunya,
               A ɗakinka jaki ya zage ka.

A ce wai kiyashi cikin rami,
              A zaga gari ya fi hankaka!

A murya a ce kurkudun daji,
              A kan bishiya ya fi gauraka!

Wajen kwarjini wai a ce taure,
              Yana ɗara zaki a bar shakka!

A ce kai mutum duk tunaninka,
              Biri wai a can dawa ya fika!

A tashi a ce maka ɗan bebe,
              Yana zarce tsuntsu kana ɗauka?

A ce maka ɗan jinjirin mako,
               Kawai ga shi ya tashi ya bi ka!

A ce ga shi zaki yana ruri,
              Kawai ƙwa na kwaɗo ya kore ka!

Idan ban da an raina wayonka,
              Ta yaya aboki da girmanka!

A ce maka ga wani inhihi,
               Na jikanka wai shi ya haife ka!

Dila inda yak kai wajen tsiwa,
               Yana ce da zaki ina ƙin ka?

Ta yaya a ce ga ka ga malam,
              Ka ce jahili zai ƙare ka?

Kawai dan an ace da kai zaki,
               Su karkanda sai su ji tsoronka?

Idan ban da wauta da shashanci,
              Ta yaya taɓo zai riƙe dirka?

Ta yaya a zafin wajen harbi,
              Duwu a gama shi da cinnaka?

Zaman nan da sake a dai duba,
              Idan babu taki ana shuka?

Idan ba ruwa rayuwar jama’a,
              Ina za ta je ko akwai iska?

Idan ba abinci ina homa?
              Idan ba kuɗi wa yake harka?

Da niyya ka cinna wuta ɗaki,
              Ka ce masu fetir su zo gunka!

Idan garwashi an zubar a ƙasa,
              Idanunka sun gan shi, ka taka?

Idan wani zai ba ka rumbunsa,
              Yana ce da kai ka kashe kanka?

Kawai dan gudun kar a zage ka,
              Kana ƙin fita tallafin kanka?

Ganinka batun nan na wasa ne?
               Kana ƙin nasihar masoyinka?

Abin ya wuce hira ko bilhu,
              Ku tauna da kai da maƙotanka.

Idan har ƙilu za ta jawo bau,
              Su Tijjani ƙwayar suke ɗauka.

Ka dinga kuka kar ka sha guiɓa,
               Kwalweniya kart a ɗauke ka.

Aboki ka ɗau gaskiya ka riƙe,
              Ka lura da duk masu ƙaunarka.

 

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub