Hausa Ba'a

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hausa KirariHausa Ba'a


Ba’a, na ɗaya daga cikin rassan adabin bakan Hausa wacce ke cikin rukunin azancin zance. Ba’a, salo ce ta iya magana da Hausawa kan yi amfani da ita a gurare da dama dan bayar da dariya. tana ɗaya daga cikin salon da wasu daga cikin makaɗan ban-dariya ke amfani da ita wajen bayar da dariya.

Yahaya, Zariya, Gusau da ‘Yar’aduwa (1987), sun bata ma’ana ta cewa, “Magana ce wadda ake yi wa abokin zance ko taɗi da niyyar raha don a ji daɗin zance ko da niyyar shammata don a yi dariya. Wani lokaci ba’a kan ɓata ran wanda aka yi wa ita”.

Shi kuwa Farfesa Ɗangambo (1984), ya basu aji ɗaya ne tare da baƙar magana, inda ya ce, “Ba’a da baƙar magana, maganganu ne da kan ɓata rai ga wanda aka yi wa”.

Kenan, bisa la’akari da waɗannan ma’anoni guda biyu, ba’a, tana ayyuka biyu; faranta rai ga mai sauraro, da kuma ɓata rai ga wanda aka yi wa. Amma kuma a al’adance, aikin faranta ran ya fi yawa. Misali a yanayin da uba ya yi wa ɗansa ba’a, za a taras cewa da uban da ɗan duk sun samu nishaɗi, haka ma tsakanin miji da mata, haka tsakanin saurayi da budurwa, haka nan ma tsakanin abokai, da sauransu. Sai dai wani abun lura shi ne cewa salo da kuma irin kalar ba'a shi ke maisheta ta ɓata rai ko ta saka raha. Misali, faɗin mai gambara wuya siriri kamar damtsen tsuhowar da ta shekara ba lafiya wannan zai iya harzuƙa mutum.

Haka nan kuma bayan aikin raha da ɓata rai da ba'a ke yi, tana taimakawa wajen yi wa mutum nuni da barin aikata abun da bai kamata ba. Misali, idan ana cikin zance sai aka ji wani ya fiye magana da yawa, to na gaba da shi zai iya ce masa, ka fiye surutu kamar kabari. Jin wannan shi kuma za ta saka ya ɗan tsagaita.

Dukkan rukunin mutane, manya da yara, maza da mata sukan yi ba’a dan a yi raha. Amma Farfesa Ɗangambo (1984), ya ce mahauta (masu sana’ar fawa) sun fi iya ba’a. har ma ya kawo wannan ɗan gajeren labarin dan tabbatar da haka:

Wata rana, wani mutum ya je wurin wani mahauci zai sayi tsire, ya dubi tsiren, ya ce, “Kai, malam, wannan naman ya gasu kuwa?” Sai mahaucin ya dube shi, ya ce, “A’a, ai yawo take yi”. Wato yana nufin dabbar ma ba a riga an yanka ta ba tukuna, ƙarewar ɗanye kenan ko rashin gasuwa.

Ana yin ba’a ne a duk lokacin da ta kama, babu wani keɓantaccen wuri ko lokaci ko biki da ake yin ba’a. Makaɗan ban-dariya kan yi ba’a a lokacin da suke gudanar da sana’arsu ta kiɗa, haka ma mahauta sukan yi ba’a a lokuta da kuma guraren da suke gudanar da sana’o’insu, mahaifi kan yiwa ‘ya’yansa ba’a a duk lokacin da ta kama, miji kan yiwa matarsa ba’a, samari kan yiwa junansu ba’a a lokutan hira da sauransu.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub