Hikaya: Mutum da Kifi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hikaya: Mutum da Kifi

Gabatarwa

Wata rana a wani gari, wani attajiri ya aiki yaronsa ya je ya sayo masa kifi. Ko da mutumin nan ya je gurin sayen kifin nan sai ya taras da layi; jama'a sun yi yawa a wajen. Sai ya jira har wani lokaci, jama'a kuma sai ƙara yawa su ke, wannan ya zo, wancan ya tafi.

Mutumin nan dai jira ya ke yi, amma har yanzu bai samu kifi ba. Can kuma mai gidan nasa yana jiran sa, ya kuma san in har bai samu kifin nan ba akwai matsala. Gashi ya ɓata lokaci, to yanzu idan ya koma me zai ce da mai gidansa?

Yana nan yana jira, sai ya ga kifi ya kusa ƙarewa. Can sai wata dabara ta zo masa, sai ya riƙa ɗaukar kifayen nan yana shinshina/sinsina wa. Da mutane suka ga haka sai suka ce ba za su sayi kifin da aka saka a hanci ba. Shi kuma mai kifi da ya ji haka sai ya rufe mutumin nan da faɗa yana mai cewa: "Ai ga irin ta nan, ka kore min masu ciniki, ni kuma sauran kifina kenan. Sai ka biya ni kuɗin kifina". Da mutumin nan ya ji haka sai ya ji daɗi a ransa, amma bai nuna a fili ba don kar a gane shi.

Sai ya ce da mai kifi, "Ni fa ba a hanci na ke saka wa ba, magana muke yi da su, ina tambayar su ne game da wani ɗan'uwana da ya faɗa ruwa jiya ko sun gan shi". Cikin mamaki sai mai kifi ya ce da shi "To wacce irin amsa suka baka?" Sai mutumin ya ce: "Sun ce ba su da masaniya game da shi, saboda su rabon su da ruwa tun makonni biyu da suka wuce". Daga ƙarshe aka gaya masa kuɗin kifi, shi kuma ya ƙirga ya biya, aka ƙunshe masa kifi a leda ya karɓa ya kai wa mai gidansa.


Ana iya turo labari domin a wallafawa ta:
Was-af: 0803 964 8244 (+234803 964 8244)
Imel: rumbunilimi@gmail.com


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub