Makaɗan Sana'a

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Makaɗan Sana'a


Gabatarwa

Makaɗan sana’a su ne makaɗan da suke yiwa masu sana’ar gargajiya kiɗa da waƙa. Akwai cuɗanya tsakanin makaɗan maza da makaɗan sana’a.

Wasu daga cikin makaɗan maza, su ne makaɗan sana’a, saboda wasu sana’o’in dama can na jarumtaka ne, misali, farauta na daga cikin sana’o’in gargajiya na Bahaushe, kuma kiɗan farauta kiɗan maza ne, saboda haka ya zamo kiɗan sana’a kenan.

Idan kuma muka ɗauki kokawa da dambe, wasanni ne na nishaɗi da jaruman maza ke yi don gwada jarumtakarsu da kuma burge jama’a. To ita kokawa yawanci manoma ke yi, shi kuma dambe, mahauta ke yi.

Daga cikin irin makaɗan da ke kiɗan maza kuma suna na sana’a akwai Ɗan’anace da yake kiɗan dambe (kiɗan maza) sannan kuma yana kiɗan noma (kiɗan sana’a), sai kuma Isan Ɗanmakaho da yake kiɗan noma (kiɗan sana’a) sannan kuma yana kiɗan kokawa (kiɗan maza), da sauransu.

Dukkan sana’o’in Hausawa na gargajiya, suna da makaɗansu, wasu sano’in ma, su masu sana’ar ne su ke rikiɗewa su zama makaɗanta kamar ƙira da wanzanci.

Rabe-Raben Makaɗan Sana’a

Bisa la’akari da irin sana’o’in da ake da su, sai Zarruƙ, Kafin Hausa da Al-Hassan (1987), suka karkasa makaɗan sana’a zuwa rukunai biyu kamar haka:

  1. Makaɗan Sana’ar Tattalin Arziƙi: A wannan rukuni akwai makaɗan noma, fawa, ƙira, da wanzanci.
  2. Makaɗan Sana’ar Maza (wato makaɗan maza kenan kai tsaye): Makaɗan dambe (shi dambe wasa ne mahauta), makaɗan kokawa, makaɗan farauta (Ita farauta sana’a ce, sannan kuma jarumi ne ke yinta, saboda haka makaɗin farauta zai iya shiga cikin ajin makaɗan sana’a da kuma ajin makaɗan maza), makaɗan shanci, da sauransu.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub