Hausa Take

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Take


Gabatarwa

Take kiɗa ne ko busa da makaɗa kan kaɗa ko su busa wa wani mutum; yawanci masu sarauta ko sarautar kanta ko kuma wani jarumi, ko wani gari, da sauransu. Haka nan ma samari da ‘yan mata akan kaɗa musu take musamman a lokutan rawar kalangu. Makaɗan maza, makaɗan fada, makaɗan sarauta da makaɗan jama’a, su suka fi yin take.

Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992), sun siffanta take da cewa, “Take ɗan guntun amo ne da ake kaɗawa ko busawa da kowane irin abin kiɗa ko busa ba tare da waƙa ba. Amma masu kaɗa taken da waɗanda ake kaɗawa sun san abin da ake nufi da inda aka dosa da shi”.

Take yana keɓanta ne da wanda aka yi taken dominsa ne shi kaɗai rak! Wanda ka iya zama mutum ɗaya, ƙungiya, ko kuma wani gari da saraunsu. Matuƙar aka ƙirƙiri take, aka kaɗawa wani shi, to, ba dama kuma a yi amfani da wannan taken ga wani mutum dabam ba shi ba.

Ana yin take ne da abin kiɗa ko busa, sannan kuma a bishi da magana domin mai sauraro ya fahimci abin da ake nufi da inda aka dosa. A wasu lokutan shi kansa kiɗan ko busar magana ce wanda sai mai yi da wanda ake yi wa suka fi ganewa. Amma akan samu wani maroƙi a irin wannan halin ya riƙa faɗin abin da ake kaɗawa ko busawa in har kiɗan ko busar na magana ne. A yanayin kiɗa akan samu makaɗin yana kaɗawa sannan kuma yana faɗin abin da yake kaɗawa, amma  busa ba wannan damar dole a samu mai yin magana dabam, kodayake shima kiɗa wasu lokutan akan samu mai kiɗa dabam, haka nan ma mai faɗin maganar dabam. Akwai kuma taken da zallar kiɗa ne ko busa; abin nufi, kiɗa ne kawai ko busa ba wata magana ake faɗi a cikin kiɗan ko busar ba.

Akwai dangataka tsakanin take da kuma kirari a wasu lokutan. Kasancewar take kiɗa ne, to idan aka kaɗawa mai shi, musamman jarumai kamar masu dambe, kokawa, farauta da sauransu, sukan taso suna kirari. Wannan gaɓar ita ta haɗa take da kirari. Amma kowanne daga cikinsu gashin kansa yake ci. Shi take kiɗa ne, shi kuwa kirari magana ce.

Take wani abu ne mai matuƙar muhimmanci a Ƙasar Hausa. Saboda muhimmancinsa har ana gadonsa. Sai dai idan take na gado ne za a ji a cikinsa ana cewa, An sare ƙaya, ƙaya ta tofo, ko kuma Kyawun gida da magaji, ko kum Kyawun ɗanƙwarai ya gaji uba nai da sauransu. A cikin take akwai fa’idojin da suka haɗa da zaburantarwa, ƙarfafar guiwa, taskace tarihi da al’adu, sarrafa harshe, fasaha, da sauransu.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur, Kano – Nigeria.

Junaidu I. da ‘Yar’aduwa T.M. (2002). Harshen da Adabin Hausa a Kammale don Manyan Makarantun Sikandire. Spectrum Books Limited. Najeriya.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub