Hausa Zambo

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zambo


Gabatarwa

Zambo, salon magana ne da ake amfani da shi wajen baƙantawa mutum ta cikin hikima, ta hanyar bayyana siffofinsa sannan kuma a danganta shi da aikin da ya aikata na muni. Wato a cikin zambo ana fito da surar mutum ne a fili, sannan kuma sai a munana shi ta hanyar bayyanar da ɓoyayyen mummunan aikin da ya aikata. Akan siffanta mutum matuƙa gaya, ta yanda duk wanda ya san shi, da ya ji zai gane  wanda aka nufa da wannan magana.

Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992),  suka ce, “Kalmomi ne na ɓatawa da ake amfani da su don a musguna wa wani. Akan kwatanta kama ko hali ko ɗabi’a da wasu munanan siffofi ko halaye don a wulaƙanta mutum”.

Zambo zagi ne. Farfesa Ɗangambo (1984), ya ce “zambo zagi ne na kai tsaye, idan an kwatanta shi da habaici”. Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992), sun bayyana cewa wasu sun ɗau zambo zagi ne kuma kishiyar yabo.

Kenan za mu fahimci cewa akwai dangantaka tsakanin zambo da habaici. Idan muka so ma muna iya cewa, wa da ƙani su ke, bisa dogaro da jawabin Farfesa Ɗangambo (1984), da ya zo a sama. Wato a bayyane, da zambo da habaici duka zagi ne a ra’ayin Farfesa, sai dai shi habaici ana sakaya wa, ba kowa zai gane wanda ake zagi ba. Amma a cikin zambo, duk wanda ya san wanda ake zagi, to da ya saurari wannan zambon zai gane shi. Saboda haka shi zambo, wan habaici ne.

Ana yin zambo saboda dalilai masu yawa, daga ciki akwai:

  1. Ƙiyayya tsakanin mutane kan jawo a yi zambo don a rage wa wanda ake ƙi daraja a cikin mutane, ko a jawo jama’a su ƙi shi. Wannan kuma akan fake da wani aibi da mutum ya aikata komai ƙanƙantar sa, sai a kambama shi, a kururuta shi yadda abin zai yi muni sosai. Dubi waƙar Mamman Shata ta Gagarabadau. In da ya ke ce da shi “…shadidi, mazinaci…”.
  2. Son fifita wani sama da wani. Kamar abin da ya shafi sarakuna, mawaƙansu kan yi zambo su ɓata ‘yan’uwansu dan dai su mawaƙan su sami ɗaukaka a gurin sarakunan, sannan kuma su jawo wa shi ɗayan baƙin jini  a cikin jama’a. Dubi waƙar Sani Aliyu Ɗandawo ta Turaki Aminuwan Maza gurin da yake cewa: “‘Yan sarki sun raina mutane, ‘yan sarki sun raina mawaƙa, sun mai she mu ba mu san komai ba, in za su ba mu kyautar doki, wai su ramamme suka ba mu, ko wanda bai gani…”.
  3. Sannan ana yin zambo da nufin gargaɗi ko jan-kunne, ko ankarar wa, da sauransu.

Haƙiƙa akwai gwanintar harshe a cikin zambo, saboda duka ne ba kama suna. Ana amfani da wannan gwaninta ta harshe a yi raga-raga da mutuncin mutum, kuma ba dama ya fito ya yi magana, saboda ba a kama suna ba. Dan haka da zarar ya ama, to ya bayyana kansa kenan. Caɓ-ɗi-jam! Wani aikin sai Hausa.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub