Tsarin Sauti: Furucin Baƙaƙe Masu Goyo

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tsarin Sauti: Furucin Baƙaƙe Masu Goyo


Gabatarwa

Furucin baƙaƙe masu goyo hawa biyu ne, ana yi wa furucin baƙin farko goyon da furucin baƙi na biyu. Wato bayan an furta baƙin farko, sai kuma a goya masa furucin baƙi na biyu su fito tare.

Leɓantaccen Bahanɗe

Suna ne na baƙin da ake fara wa da yin furucin hanɗawa, sannan kuma a goyo shi da furucin leɓawa ta hanyar kewaye laɓɓan. Baƙaƙen su ne /kw/, /ƙw/ da /gw/.

  1. /kw/ kamar a cikin kalmomin kwakwa, Dakwa, Lakwaya, kwashe, Kwatarkwashi da makamantan su.
  2. /ƙw/ kamar yadda take zuwa a cikin kalmomin ƙwaya, lanƙwasa, ƙwaƙwalwa, daƙwalwa, ƙwai da makamantan su.
  3. /gw/ kamar yadda take zuwa a cikin kalmomin lagwada, Gwanja, gwanda, gwagwaruma, gwaɓi da makamantan su.

Ganɗataccen Bahanƙe

Suna ne na baƙin da doron harshe yake haɗewa da hanɗa sannan kuma sai gaban harshe ya ɗaga sama doshi ganɗa. Baƙaƙen su ne /kj/, /ƙj/ da kuma /gj/.

  1. /kj/ alama ce ta furucin /kya, kamar yadda yake zuwa a cikin kalmomin kyanwa, kyakkyawa, kyarma, kyauta, kyamara da makamantan su.
  2. /ƙj/ alama ce ta furucin /ƙy/, kamar yadda take zuwa a cikin kalmomin ƙyaure, ƙyama, ƙyanda, ƙyasbi, ƙyalƙyali da makamantan su.
  3. /gj/ alama ce ta furucin /gy/, kamar yadda take zuwa a cikin kalmomin gyale, gyatuma, gyartai, gyauro, gyauto da makamantan su.

Ganɗatacciyar Hamza

/Ɂj/ alama ce ta furucin /’y/, kamar yadda take zuwa a cikin kalmomin ‘ya’ya, ‘yanci da sauransu.

Ganɗataccen Baleɓe

/Φj/ alama e ta furucin /fy/, kamar yadda take zuwa a cikin kalmar fyacewa.

Manazarta:


Junaidu I. da ‘Yar’aduwa T.M (Babu Shekara). Harshe da Adabin Hausa a Kammale Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Nigeria.

Sani M.A.Z. (2007). Tsarin Sauti Da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Sani M.A.Z., Muhammad A. Da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Langugae Don Masu Rubuta Jarabawar WASC da SSCE. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M da ‘Yar’aduwa T.M. (2006). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub